Ƙasar India ta rattaba hannu kan wata muhimmiyar yarjejeniya da Brazil domin haɗin gwiwa kan ma’adanai masu muhimmanci, da nufin rage dogaronta ga kayayyakin da ake samu daga China.
Yarjejeniyar na mayar da hankali ne kan samun ma’adanai da ake amfani da su a fannoni na fasaha kamar na’urorin lantarki, makamashin sabuntawa, da motocin lantarki. Jami’an Indiya sun ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen bincike, hakar ma’adanai, sarrafawa, da kuma gina hanyoyin samar da su tsakanin ƙasashen biyu.
Hukumomin Indiya na kallon wannan mataki a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin samun albarkatun ƙasa da kuma kare tsaron tattalin arzikinta da fasaharta na dogon lokaci. Ita ma Brazil ana sa ran za ta amfana ta hanyar karin jarin waje da bunƙasar ciniki.
Masana sun ce ƙasashe da dama na duniya suna neman sabbin hanyoyin samun ma’adanai masu muhimmanci, yayin da gasa ke ƙaruwa kuma ake fargabar dogaro da ƙasa guda ɗaya wajen samar da su.