Iran ta ce ba ta da wani shiri a halin yanzu na bai wa Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) damar binciken cibiyoyinta na nukiliya da suka lalace sakamakon yaƙi.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghaei, ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai, inda ya ce babu wata yarjejeniya da ta tanadi irin wannan batu.
Ya ce Iran za ta ci gaba da bin tsarin da take amfani da shi a yanzu a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) da kuma dokokin kulawa da makaman nukiliya.
“Gaba ɗaya babu wata doka ko tsari a kan wannan batun. A matsayinmu na mamba a yarjejeniyar NPT, za mu ci gaba da bin hanyoyin da muke kai yanzu, kuma tsarin a bayyane yake,” in ji Baghaei.
Hakazalika, ya ce babu wata ganawa da aka shirya tsakaninsa da babban daraktan IAEA, Rafael Grossi, a Switzerland.
Wannan bayani na Iran ya zo ne bayan kalaman Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, wanda ya bayyana cewa Iran ta amince a ba masu binciken damar bincikar cibiyoyin nukiliyarta.
Sai dai gwamnatin Iran ta musanta wannan ikirari, tana mai cewa ba ta ɗauki wani sabon alƙawari dangane da batun binciken nukiliya ba, kuma hulɗarta da IAEA za ta ci gaba ne a ƙarƙashin dokokin da ake da su.