Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya naɗa jigo a jam'iyyar African Democratic Congress (ADC), Kenneth Okonkwo, a matsayin kakakinsa, makonni kaɗan bayan ɗan siyasar ya soki zaɓin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar domin zaɓen shekarar 2027.Okonkwo, wanda tsohon jarumi ne a masana'antar fina-finai, ya sanar da naɗin nasa ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, inda ya gode wa Atiku bisa amincewar da ya nuna masa.
Ya ce, "Ina bai wa Allah ɗaukaka bisa naɗa ni da Mai Girma Atiku Abubakar ya yi a matsayin kakakinsa. Ina matuƙar godiya bisa irin amincewar da ya nuna gare ni."
Okonkwo ya bayyana cewa wannan naɗi ya nuna irin salon jagorancin Atiku, yana mai cewa maimakon ya fusata idan wani daga cikin na kusa da shi ya bayyana damuwa kan wani mataki da aka ɗauka, Atiku yakan zaɓi tattaunawa da sasanci domin samar da mafita.
Ya kuma bayyana cewa, a wata ganawa da suka yi da Atiku da sauran shugabannin ADC, an tattauna batun muradun yankin Kudu maso Gabas, tare da ba da tabbacin kare muradun yankin duk da ƙalubalen da Dokar Zaɓe ta 2026 ta haifar.
Haka kuma, Okonkwo ya miƙa godiyarsa ga Dr. Kashim Imam, tsohon Shugaban Jam'iyyar ADC Ralphs Nwosu, da Babban Mataimaki na Musamman ga Atiku kan Ayyuka na Musamman, Dr. Ekene Onwuka, saboda rawar da suka taka wajen ƙarfafa jam'iyyar gabanin zaɓen 2027.
Ya kuma gode wa iyalansa, magoya bayansa da abokansa bisa addu'o'i da goyon bayan da suka ba shi, yana roƙon su da su ci gaba da yi masa addu'ar samun hikima, jaruntaka da kariya wajen gudanar da sabon nauyin da aka ɗora masa.
Naɗin Okonkwo ya zo ne bayan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan zaɓin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC, inda ya yi gargaɗin cewa zaɓen mutum daga yankin Kudu maso Kudu zai ƙara tauye damar yankin Kudu maso Gabas wajen samun wakilci a manyan muƙaman ƙasa.
A cewarsa, idan aka zaɓi ɗan takara daga Kudu maso Kudu a matsayin mataimaki, hakan zai ci gaba da hana yankin Kudu maso Gabas samun kujerar shugaban ƙasa ko mataimakinsa, lamarin da ya ce ya daɗe tun daga shekarar 1999.
Daga bisani, jam'iyyar ADC ta zaɓi tsohon Gwamnan Jihar Rivers kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar bayan Atiku ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen fidda gwani na ƙasa baki ɗaya.