Harin Sojojin Rasha A Ukraine Ya Kashe Wata Daliba Yar Nijeriya Kwanakin Kadan Kafin Ta Kammala Karatu

Wata dalibar likitanci 'yar Najeriya, Nnani Adaobi Marian, ta rasu bayan ta jikkata sakamakon harin sama da sojojin Rasha suka kai a birnin Kharkiv na ƙasar Ukraine, kwanaki kaɗan kafin ranar da za ta kammala karatunta.

Nnani Adaobi

Rahotanni sun ce harin ya faru ne a ranar 29 ga Yuni, inda aka jefa bama-bamai a yankin Kholodnohirskyi na Kharkiv. Harin ya yi sanadin mutuwar mutane 14 a yankunan Dnipropetrovsk, Zaporizhzhia da Kharkiv, yayin da wasu 98 suka jikkata.

A cikin wata sanarwa da Jami'ar Kharkiv National Medical University ta fitar, ta bayyana cewa Marian ta samu munanan raunuka a harin, kuma duk da ƙoƙarin likitoci a Ukraine da Jamus na ceto rayuwarta, daga bisani ta rasu.

Jami'ar ta ce Marian ta fara karatu a shekarar 2020, inda ta yi fice wajen ƙwazo da samun sakamako mai kyau a karatu. Haka kuma ta halarci shirye-shiryen horaswa na ƙasa da ƙasa, ciki har da a Jami'ar Cambridge a shekarar 2024 da kuma Biruni University a 2025 domin ƙara ƙwarewa a fannin likitanci da binciken kimiyya.

Sanarwar ta bayyana Marian a matsayin mai hazaka, kirki da son taimakon jama'a.

Rahotanni sun kuma nuna cewa Marian na tare da kawarta, Fatima Huseynova, ne domin ɗaukar hotunan bikin kammala karatu lokacin da harin ya auku. An shirya ba su takardar shaidar kammala karatu washegarin ranar.

Fatima ta mutu nan take a harin, yayin da Marian ta samu munanan raunuka kafin daga bisani ta rasu a asibiti.

An kuma rwwaito cewa ɗaya daga cikin bama-baman ya fashe a kan wata hanya a yankin Kholodnohirskyi, lamarin da ya jikkata wasu mutum 12.

Post a Comment

Previous Post Next Post