Iran Ta Gargadi Amurka Game Da Mashigar Hormuz

Iran ta gargadi Amurka da cewa za ta fuskanci "mummunan sakamako" bayan sabbin hare-haren sama da aka ce Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin kai wa, tana mai jaddada cewa mashigin ruwan Hormuz zai ci gaba da kasancewa a buɗe ne kawai bisa sharuddan da Tehran ta gindaya.

Iran Da Amurka

Amurka ta ce ta kai hare-haren ne domin rage barazanar da Iran ke yi ga jiragen kasuwanci da ke zirga-zirga ta mashigin Hormuz, bayan zargin da ta yi wa Tehran na kai hare-hare kan wasu jiragen ruwa.

Sai dai jami'an Iran sun yi Allah wadai da hare-haren, suna masu cewa sun keta ikon ƙasarsu, tare da yin barazanar ɗaukar fansa. Sun kuma ce zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin Hormuz za ta kasance karkashin sharuddan da Iran ta shimfiɗa.

A nasa bangaren, Shugaba Donald Trump ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a baya ta kare, yana mai gargadin cewa Amurka za ta sake ɗaukar matakin soja idan Iran ta ci gaba da kai hare-hare kan jiragen kasuwanci ko muradun Amurka a yankin Gulf.

Rahotanni sun ce Iran ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan sansanonin sojin Amurka da ke Bahrain, Kuwait da Qatar. Ita kuwa Amurka ta ce ta lalata wasu wuraren sojin Iran, ciki har da ma'ajiyar makamai masu linzami da cibiyoyin rundunar ruwanta.

Mashigin Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin safarar ɗanyen mai a duniya, inda kusan kashi 20 cikin 100 na man da ake safararsa a duniya ke bi ta wannan hanya.

A halin da ake ciki, Majalisar Ɗinkin Duniya da wasu ƙasashen yankin Gulf sun yi kira ga Amurka da Iran da su nuna haƙuri tare da komawa teburin tattaunawa domin kauce wa rikicin ya rikide zuwa babban yaƙin yanki.

Post a Comment

Previous Post Next Post