Shugaban Kasar Nijeriya Bola Ahmed Tinubu Ya Yi Afuwa Ga Mutune 78 Da Aka Kama Saboda Jifarsa Da Suka Yi A Abuja

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin sakin mutane 78 da aka kama bisa zargin hannu a harin da aka kai wa ayarinsa a Garki, Abuja.

Bola Ahmed Tinubu

Rundunar ’yansandan babban birnin tarayya Abuja ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakinta, Josephine Adeh, ta fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce an kama mutanen ne bayan wasu matasa sun jefe ayarin motocin shugaban ƙasar da duwatsu da wasu abubuwa masu haɗari a ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026, jim kaɗan bayan Tinubu ya idar da sallar Juma’a a wani masallaci da ke unguwar Garki.

Lamarin ya yi sanadin lalacewar wasu motoci tare da jikkata jami’an tsaro.

Ta ce bayan kama mutum 78, fadar shugaban ƙasa ta bayar da umarnin a yi musu afuwa, a gargaɗe su sannan a sake su.

A cewar sanarwar, rundunar ’yan sandan ta fara aiwatar da matakan da suka dace domin sakin waɗanda ake zargin.

Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Ahmed Mohammed Sanusi, ya gargaɗi jama’a da su guji tashin hankali, tayar da zaune tsaye da lalata dukiyoyin jama’a, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

Ya kuma buƙaci ’yan siyasa da magoya bayansu su rungumi siyasa cikin lumana tare da kauce wa kalaman tunzura jama’a da duk wani abu da zai iya haddasa rikici.

Post a Comment

Previous Post Next Post