Zan Cire Dukkan Ma’aikatan Jihar Katsina Daga Tsarin PENCOM da Aka Kakaba Su Idan na Kai ga Mulki

Ɗan takarar Gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Ɗan Marke ya tabbatar wa da Ma’aikatan jihar Katsina cewa zai cire su daga tsarin taimakekeniya na fansho da Gwamnati mai ci a yanzu a sanya su, domin su samu kuɗaɗe masu yawa bayan ajiye aiki.

Sanata Yakubu Lado Ɗan Marke ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓensa da ya wakana jiya a cikin birnin Katsina.

Sanata Yakubu Lado Ɗan Marke ya nanata cewa, zai kuma tabbatar da ya ba da kula ta musamman a ɓangren lafiya tare da bayar da magunguna kyauta ga duk wani ɗan jihar Katsina da ya je asibiti.

“Saboda katin Naira ɗari 200 ko maganin dubu 1000 sai marar lafiya ya rasa ransa, to idan Allah ya kai mu ga nasara zan tabbatar an kula da mutane kyauta a Asibitocin jihar” Inji shi.

Lado ya kuma bayyana cewa, zai gina manyan Asibitoci guda uku, a duka shiyyoyin jihar domin hana 'yan jihar Katsina fita waje neman lafiya.

Ya ƙara da cewa, duk da cewa an baiwa jihar Katsina Naira tiriliyan 3 daga Gwamnatin tarayya amma har yanzu ɓangaren ilimi a lalace yake a jihar, inda ya bayar da tabbacin kawo gyara a ɓangaren na musamman, ga abin da ya ce.

“Zan tabbatar da ilimi kyauta a jihar Katsina duba da yadda komai ya taɓarɓare, domin ko jarabawar bana da aka gudanar jihar Katsina ce ta zo ta ukun ƙarshe”.

Ya sake bayyana ƙudirinsa na inganta rayuwar mata da kuma samar da shirin koyar da sana’o’i domin inganta rayuwar 'yan jihar Katsina.

Dangane da batun tsaro kuwa, ya jaddada cewa idan har aka zaɓe shi a cikin ƙanƙanin lokaci zai kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta ke addabar jihar Katsina da salwantar da rayuwar al’umma ba gaira ba dalili.

Post a Comment

Previous Post Next Post