Ana gudanar da zanga-zanga a birane daban-daban na faɗin Spain, lamarin da ya janyo cikas ga tafiye-tafiye da harkokin sufuri a ƙasar.
Wannan ne yajin aikin gama-gari na farko da aka yi a kasar cikin shekaru 14, inda ƴansanda suka kama masu zanga-zanga da dama a arangamar da suka yi a safiyar yau.Wakilin BBC ya ce an ga yadda aka katse tafiye-tafiye, mutane da dama sun kauce wa yin balaguro ta jiragen kasa, a cikin gari ma tituna sun yi tsit ba mutane.
Ƙungiyoyin ƙwadago da masu rajin kare haƙƙin jama'a a Sifaniya sun dade suna neman gwamnati ta ɗauki matakan magance matsalar tsadar gidaje, wadda ta haddasa tashin farashin kuɗin haya.