Kungiyar Yankin Arewa Ta Tsakiya Ta Gargadi APC, PDP, ADC: “Ku Ba Mu Shugabancin Kasa, Ko Ku Rasa Kuri’unmu”


Kungiyar ta bayyana cewa manyan jam’iyyun siyasa  ciki har da jam’iyya mai  mulki  (APC), (ADC) da kuma (PDP)  za su rasa kuri’u daga shiyyar idan suka ƙi amincewa da wannan buƙata.

Yayin taron manema labarai a Abuja a ranar Juma’a, wanda shugaban ƙungiyar kuma wanda ya kafa ta, Farfesa K’tso Nghargbu, ya jagoranta, NCRM ta kuma yi kira ga sauran shiyyoyin ƙasa da su mara wa Arewa ta Tsakiya baya a neman shugabancin ƙasa.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ƙungiyar ta dage da cewa tun bayan samun ‘yancin kai shiyyar Arewa ta Tsakiya ba ta taɓa samar da shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa ba, don haka ya dace a ba ta dama a 2027. Wannan shiyya ta ƙunshi jihohi Neja, Kogi, Benuwai, Filato, Nasarawa da Kwara, tare da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Farfesa Nghargbu ya ce Arewa ta Tsakiya tana da wadatattun ƴan siyasa da za su iya magance matsalolin shugabanci da ƙasar ke fama da su, musamman a lokacin da ake ganin ƙaruwar ɓacin rai tsakanin manyan ’yan siyasa na arewa da takwarorinsu na kudu.

Ya ƙara da cewa, banda gogaggun ’yan siyasa da shugabanni kamar Dr. Gbenga Olawepo Hashim daga jihar Kwara, wanda ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 ƙarƙashin PDP, akwai wasu manyan jiga-jigai daga yankin da za su shiga takarar.

Ya ce:
“Mun ga ya zama wajibi, nauyi gare mu a matsayin amana ga jama’armu, mu sake jaddada cewa shiyyar Arewa ta Tsakiya tana neman, tana roƙo, tana buƙata cewa manyan jam’iyyun siyasa su ɗauki ɗan takara daga wannan shiyya don kujerar shugaban ƙasa.

“Wannan yana da muhimmanci duba da yadda ake ƙara samun rashin jituwa, ƙiyayya da shakku tsakanin manyan ’yan siyasa na arewa da na kudu. Arewa ta Tsakiya ce mafita mafi dacewa wajen haɗin kan ƙasa.

“Muna kira ga sauran shiyyoyi guda biyar, musamman manyan jam’iyyun siyasa a Najeriya, da su ba wa mutanen Arewa ta Tsakiya wannan dama. Muna faɗin haka ba don barazana ba, sai don amana ga ƙasar nan mai girma, ba tare da cutar da cigaban ƙasa ba.

“Muna faɗin haka a sarari: duk jam’iyyar da ta raina mu, za mu raina ta da kuri’unmu. Amma jam’iyyar da ta girmama mu, ita ce za ta more ƙuri’unmu. Muna fatan mun isa wajen lamarin siyasar Najeriya, wacce ke buƙatar kwanciyar hankali, zaman lafiya, da wadata.”

Haka kuma, Farfesa Nghargbu ya bayyana goyon bayan ƙungiyar ga ƙoƙarin shigar da ’yan takara masu zaman kansu a kundin tsarin mulkin Najeriya, yana mai cewa hakan zai ba da dama ga waɗanda jam’iyyu suka ƙi bayar da tikiti sai su tsaya da kansu.

Ya ce:
“Tsarin ’yan takara masu zaman kansu ɗaya ne daga cikin hanyoyin da za su taimaka wa Najeriya wajen daƙile yawan zaluncin ƴan siyasa masu son kuɗi. Don haka Arewa ta Tsakiya tana goyon bayan wannan gyara a tsarin mulki.”

Post a Comment

Previous Post Next Post