Hukumar ‘Yan Sanda ta jihar Kebbi ta tabbatar da cewa an yi garkuwa da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sama’ila Bagudo, wanda ke wakiltar mazaɓar Bagudo.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ’yan bindiga da ake zargin na yankin Lakurawa ne suka kai wa ɗan majalisar hari da misalin ƙarfe 8 na yammacin ranar Juma’a, a lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida bayan idar da sallar Isha’i.
Hukumar ‘yan sandan ta bayyana cewa har yanzu ɗan majalisar yana hannun masu garkuwar, amma jami’an tsaro suna ƙoƙarin kuɓutar da shi cikin koshin lafiya.
Ta kuma tabbatar wa jama’a cewa ana ci gaba da gudanar da bincike da ƙoƙari domin ganin an ceto ɗan majalisar tare da kama masu laifin da hannu.