BAYANIN WANI LIKITA
"Mun kwantar da ita a "ward" na mata 'yan tiyata, tana shiga duk suka toshe hanci saboda mummunan warin da yake fita daga jikin ta.
Mace ce wadda ba ta wuce shekaru 35 ba, amma da ka gani za ka ga duk ta fita hayyacinta. Duk wata ƙima ta ɗan'Adam babu ita, saboda tsarguwa da take da ita.
Mun tambaye ta, shi ne take cewa ciwon ya fara da wani ɗan ƙurji a saman mama (breast), wanda ya yi ruwa, sai aka kai ta wajen mai maganin gargajiya, ya yi mata sakkiya har sau biyu.
Duk da haka babu wani cigaba, ta tambaye shi ko dai ta tafi asibiti? Ya ce ai maganin gida zai yi. Sai bayan shekara biyu jikin nata duk ya ruɓe, da ta ga lallai mutuwa za ta yi, sai ta yi wa kanta nasiha ta tafi asibiti. Tun ba a tafi ko ina ba aka tabbatar mata da cewa tana da ciwon daji (breast cancer).
An yi mata aiki, an yi nasarar cire ruɓaɓɓan maman, amma bayan an yi, sai cutar ta nuna cewa Cancer ɗin ta yaɗu kusan ko ina a jiki. A takaice dai ta zo a makare, sai dai a jira lokaci."
GARGAƊI
Kar ka/ki bari lokaci ya ƙure, da kun ji ba ku gane ba ku nufi asibiti da wur.
(world breast cancer day)
