Bayan rahotannin da ke cewa an kashe Jagoran Addinin Iran, Ali Khamenei, an kafa wata majalisa ta wucin gadi domin kula da harkokin shugabanci har sai an zabi sabon jagora kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Majalisar riƙon ƙwaryar ta kunshi shugaban kasa, Masoud Pezeshkian, wanda ke jagorantar bangaren zartarwa. Haka kuma akwai shugaban bangaren shari’a, Gholamhossein Mohseni Ejei, wanda ke daya daga cikin manyan jami’an gwamnati.Na uku a cikin majalisar shi ne babban malamin addini, Alireza Arafi, wanda aka nada a matsayin wakilin bangaren malamai a cikin majalisar. Wannan tsarin ya yi daidai da Mataki na 111 na kundin tsarin mulkin Iran, wanda ya tanadi cewa wadannan manyan jami’ai uku za su rike iko na wucin gadi har sai Majalisar Kwararru (Assembly of Experts) ta zabi sabon Jagoran Addini.
Ana sa ran Majalisar Kwararru za ta fara zaman tantancewa domin zabar sabon jagora, matakin da ka iya tasiri sosai ga makomar siyasa da tsaron Iran.