Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo bisa samun nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar a jiya Asabar, inda ya yaba wa mutanen jihar bisa gudanar da zaɓen cikin lumana.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na kafofin sadarwa, Tinubu ya kuma yaba wa ƙoƙarin da ya ce hukumar zaɓen Najeriya INEC ta yi."Ina taya mutanen jihar Anambra da jami'an tsaro da hukumar zaɓe bisa yadda aka samu nasarar gudanar zaɓen cikin lumana ba tare da samun matsala ba."
Tinubu ya ce nasarar da Soludo ya samu na nuna "cewa yana gudanar da mulki mai kyau. Gwamnan ya nuna cewa lallai ilimi na da amfani a mulki, kuma za a yi amfani da ilimi wajen magance matsalolin da mutane suke fuskanta."
Shugaban ya ce ya ziyarci jihar a watan Mayun da ya gabata domin ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnan ya yi, waɗanda ya bayyana da ayyuka masu muhimmanci da nagarta
"In yaba wa Soluo bisa yadda yake gudanar a mulki mai kyau domin ciyar da jihar Anambra gaba. Sannan ina kira gare shi da ya janyo abokan takararsa kusa domin haɗa ƙarfi da ƙarfi su ciyar da jihar gaba."