A ranar Alhamis ne Hillary Clinton za ta bayyana a gaban wani kwamitin majalisar wakilan Amurka da ke binciken laifukan mutumin nan da aka samu da aikata laifukan jima'i Jeffrey Epstein.
Kwanan nan tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka kuma ƴar takarar shugaban ƙasa ta amince tare da mijinta, tsohon shugaban ƙasa Bill Clinton, don ba da shaida ga kwamitin sa ido na majalisar.Dukansu a baya sun ƙi amincewa da buƙatar bayyana a gaba kwamitin, suna masu bayyana lamarin a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.
Hillary Clinton ta ce ba ta tuna ganawa ko magana da Epstein ba.
Mijinta, wanda ya san Epstein, ya musanta aikata wani laifi ko kuma wata masaniya kan laifukan da ya aikata.