MAYAƘAN BOKO HARAM SUN KAI HARI A ADAMAWA. Aƙalla mutum 25 ne aka kashe a wasu hare-hare guda biyu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne suka kai a jihar Adamawa da ke arewacin Najeriya kamar yadda wasu mazauna yankin suka sanar da kamfanin dillancin labarai ta AFP a ranar Alhamis.
An kai hare-haren ne a garuruwan Madagali da Hong, dake kan iyaka da ƙasar Kamaru, inda ake danganta su ƙungiyar ‘yan Boko Haram, waɗanda ke kai hare-hare a yankin tun lokacin da ƙungiyar ta fara tashe-tahsen hankula a 2009."Wani rukuni na masu bindiga da muke zaton ‘yan Boko Haram a kan babura ne suka kai hari a kasuwa inda suka buɗe wuta kan mutane, harin da ya kashe mutum 21," in ji wani jami’in gwamnatin ƙaramar hukumar Madagali ga AFP, wanda ya nemi a boye sunansa.
"Har yanzu muna bincike don neman wasu gawawwakin, saboda wasu na iya mutuwa a cikin daji sakamakon raunukan bindiga yayin da suke kokarin tsira."
Maharan sun kuma saci kayayyaki a kasuwar da suka haɗa da abinci da babura, in ji shi.
A garin Hong, mutane hudu sun rasa rayukansu, ciki har da sojoji uku, a cewar mazaunin garin Ezekiel Musa.