Shugaban ƙungiyar tattalin arzikin duniya, Borge Brende, ya yi murabus saboda alakarsa da marigayi Baamurkenan da aka samu da laifin lalata Jeffrey Epstein.
A farkon wannan watan ne ƙungiyar ta World Economic Forum ta ce tana gudanar da bincike, bayan wasu takardu da aka fitar a Amurka sun nuna cewa Brende ya ci abincin dare da Epstein, kuma ya aika masa da sako ta email da waya .Ƙungiyar ta ce a yanzu ba ta samu wasu abubuwa masu tayar da hankali ba.
Sanarwar ajiye aiki da Brende ya fitar bata ambaci sunan Epstein ba.
Ƙungiyar ita ce ke shirya taron tattalin arziki na duniya da ake yi kowace shekara a birnin Davos na ƙasar Switzerland da ke samun halatar shugabannin siyasa da na yan kasuwanci.