Gwamnatin Iran Ta Bukaci Mutanen Mashhad Su Rage Amfani Da Ruwa Saboda Karancinsa

Hukumomi a ƙasar Iran sun buƙaci mazauna birnin Mashhad, wanda shi ne birni na biyu mafi girma a ƙasar da su rage amfani da ruwan sha saboda ƙarancinsa.

Tun da farko, an sanar da cewa za a samu ƙarancin ruwa a birnin saboda matsanancin fari da ake fuskanta a wasu sassan ƙasar.

Rumbunan adana ruwan sha na birnin da ke kai ruwa arewa maso gabashi ya ja baya zuwa ƙasa da kashi uku, wanda shi ne mataki mafi muni da aka fuskanta a cikin gomman shekaru.

A farkon wannan watan ne shugaban ƙasar Masoud Pezeshkian ya yi gargaɗin cewa za a iya kwashe mutanen birnin a sauya musu mazauni idan har matsalar ta ci gaba da ƙamari, kuma ba a samu hanyar magance ta ba.


Post a Comment

Previous Post Next Post