Rayuwar Wasu Jajirtattun Kanawa Da Suka Rayu A Mabambanta Lokuta

Dukan su Kanawa ne da suka yi rayuwa a lokuta mabambanta kuma suka yi shuhura sosai saboda wasu dalilai da suka haɗa da kyakkyawar mu'amala da jama'a, taimakon al'umma da tawali'u da jajircewa da aiki tuƙuru da kyautatawa zuwa ga mutane.

Alh. Muhammad Ammani Inuwa

Duk da yake suna amsa inkiya ɗaya wato "Manaja" sai dai wannan Manajan Neja ne (wato Niger Club da Kings Garden) Kano ɗayan kuma Manajan PZ ne (Kamfanin PZ).

Ɗaya daga cikin su ya shiga sabgar siyasa har ma ya taɓa riƙe matsayin shugaban masu rinjaye (Majority Leader) a Majalisar Dokokin Tsohuwar Jihar Kano(Kano da Jigawa na yau) a lokacin mulkin Jam'iyyar PRP a Jamhuriya ta biyu da kuma muƙamin Shugaban Kwamitin Dattawa na Jam'iyyar ANPP na Jihar Kano, wato Alh. Muhammadu Ammani Inuwa. 

Sun samu waƙoƙi da kuma ambato daga Makaɗan Baka na Hausa masu yawa saboda kyautatawarsu zuwa gare su. Mafi shahara daga cikin waɗannan waƙoƙi nasu sune waƙar da Makaɗa Mamman Ganga Ganga ya yiwa ɗaya daga cikin su mai amshi "Ammani Manajan Neja" a cikin ƙarshe ƙarshen 1960s zuwa farko farkon 1970s da kuma wacce/wadda Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yiwa ɗayan inda yake cewa "Yayi shirin kabra da maza, Manajan PZ Kabiru Mado" a cikin 1980s.

Dukansu sun yi wafati a lokuta daban daban. Muna roƙon Allah SWT ya jaddada masu rahama su da sauran dukan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin. 

Waɗannan bayin Allah sune Marigayi Alhaji Muhammadu Ammani Inuwa (Ammani Manajan Neja) a gefen hagu da Marigayi Alhaji Kabiru Mado (Manajan PZ Kabiru Mado) a gefen dama.

Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) Jihar Zamfara, Nijeriya.

15/06/2026.

Post a Comment

Previous Post Next Post