"Ranad da na iske
Marafa,
Zaune a ƙofar
gidanai,
Ah! Sa'an da na iske
Marafa zaune a
ƙofar gidanai,
Ga alkyabba ya
bayas,
Rigam mulki ta Bidda
Ga kuma wandon
Kano nan,
Ga kuma doki ya
bayay,
Ga kuma sirdin ga
tumbas,
Ga alkyabba ya
bayas,
Kayan mulki
gare mu,
Sai ɗan mulki
Marafa,
Ga kuma kurɗi
a bamu,
Sai ɗan mulki
Marafa,
Ni mi zan cewa
Marafa?
Allah kiyaye Marafa
Allah ya sanya
Marafa ya bi gado na
tsoho".
Haka☝️☝️☝️ Dakta Alhaji Mamman Shata Katsina ya faɗa a faifansa na Marigayi mai girma Marafan Kwantagora Sanata Abdullahi Mu'azu Kwantagora mai amshi "Sai naje Kwantagora dan albarkam Marafa".
Alhaji Abdullahi Mu'azu Marafan Kwantagora ɗan Sarkin Sudan na Kwantagora Mu'azu ne, Malam Mu'azu kuma shi ne Sarkin Sudan na Kwantagora na 5 an kuma ɗauko shi daga garin Rijau inda yake Hakimci da laƙabin sarautar "Sarkin Bauchi" a shekarar 1961 aka yi masa Sarkin Sudan na Kwantagora, ya yi mulki har zuwa wafatinsa a shekarar 1974. Shi kuma ɗan Sarkin Sudan na Kwantagora Ibrahim ne, Sarkin Sudan Ibrahim kuma ɗan Malam Umaru Nagwamatse ne wato Sarkin Sudan na Kwantagora na farko da ya ƙirƙiri wannan masarauta kuma aka naɗa shi Sarkinta a shekarar 1859.
Sarkin Sudan na Kwantagora Malam Umaru Nagwamatse ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I /Abubakar Atiku mai Katuru ne, shi kuma Sarkin Musulmi Abubakar I /Abubakar Atiku mai Katuru ɗan Mujaddadi Shehu Usman Danfodiyo Tagammadahullah Birahamatihi ne.
Sarautar Marafa daɗaɗɗiyar sarauta ce da Cibiyar Daular Usmaniyya ta aro daga Daular Gobir da ake naɗa musamman zaƙaƙurin ɗan Sarki. Misali, a Sakkwato mai alfarma Sarkin Musulmi na 14 wato Mal. Muhammadu Mai Turare ɗan Sarkin Musulmi Ahmadu (Zaruƙu) ɗan Sarkin Musulmi Abubakar I /Abubakar Atiku mai Katuru ya na Marafan Sakkwato ne aka naɗa shi Sarkin Musulmi a shekarar 1915.
Marigayi Marafan Kwantagora Alh. Abdullahi Mu'azu mutum ne karimi da ya yi ƙoƙari matuƙa wajen riƙo da addini da kyautatawa ga al'umma sosai. Ya yi kyakkyawar mu'amala da jama'a abun da ya sanya al'ummarsa suka zaɓe shi a matsayin Wakilinsu a Zauren Majalisar Dattawa ta ƙasa a Ikko a ƙarƙashin tutar Jam'iyar NPN a Jamhuriya ta biyu(1979-1983).
A sanadiyarsa Kwantagora ta samu tagomashin baƙi ma'abota raya Al'adu musamman masarta kafin Allah SWT ya karɓi abunsa a yan shekarun baya.
Allah SWT ya jiƙan Marigayi Marafan Kwantagora Sanata Alh. Abdullahi Mu'azu da rahama shi da sauran dukan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani Alfarmar Sayyadir Rahama Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.
Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji), Jihar Zamfara, Nijeriya.
16/06/2026.
