Kafin Da Bayan Mulkin Su
Sardauna A Arewacin Nijeriya (3)
Tambayoyin da za mu iya ƙara yi suna da tarin yawa, amma muna iya taƙaitawa ga muhimmai.
Me ya sa ba mu tambayar kanmu gaskiyar abubuwan da suka faru ko mu nemi malamai da masana da littattafai da bayanai da suke ɗauke da tarihin ko mu binciko abubuwan da za su ƙara mana haske a zahiri, amma sai mu ƙunshe kai a cikin bambancin aƙida da siyasa da ƙabila mu ƙi bayyana gaskiyar lamurran? Wannan ba hanya ce mai ɓullewa ba!
Me ya sa ba za mu fasalta komi da ya faru da kuma duk waɗanda ke da hannu daga kowane sashe na Arewa ba? Alal misali, wace rawa Sardauna ya taka a lokacin mulkinsa da sauran muƙarrabansa na ciyar da Arewa gaba? Ko kuma wace rawa ya taka wajen tattake haƙƙokin talakawa, su wa aka take wa haƙƙoƙin? Shin haƙƙoki ne aka take, ko hukuncin hukuma ne ya bi ta kan su?Me ya sa?
Sauran muƙarraban Sardaunan kuma wace rawa suka taka, shin da izninsa ko yardarsa ko kuwa dai ta ƙashin kai ce? Shin shi kaɗai ne ya mulki Arewa ko kuwa da wasu da ba a kawo batun su? Su wa suka taimaka masa domin gudanar da mulkin yankin Arewa in har akwai? Wace gudunmuwa waɗannan manyan Arewa suka bayar wajen gina da tabbatar da rayuwar jin daɗi ko tauye haƙƙi ko akasin haka a wancan zamani?
Mu ɗau misalin wasu daga cikin manyan masu mulki da muƙamai a lokacin, kamar Sarkin Musulmi Saddiƙ Abubakar III (wanda ya yi mulki daga shekarar 1938 har zuwa 1988), wanda tarihi ya zo da bayanin a ƙasarsa ne aka kashe magoya bayan NEPU ('yan ɗarikar Tijjaniya?) a karo na farko a duk faɗin Arewa saboda riƙo da aƙidar gurguzu irin ta addini - shi ya sa ma ake kiran su da 'Shahidan Farko' daga masu goya wa 'yan NEPU baya, amma su hukumomin En'e a Sokoto da mutanen jam'iyyar 'Yanfisi (NPC) da Sarki ke jagoranta, sun kira waɗannan 'Shahidai' a matsayin 'Cinnaku' da suke hana mutane watayawa, ba kuma abin da ya dace da 'cinnaku' face kisa,kamar yadda aka aiwatar!
Ko mun taɓa zama muka nazarci irin gudunmuwar da Sarakunan Kano, musamman Abdullahi Bayero (daga 1926–1953) da Muhammadu Sanusi I (daga 1954–1963) suka bayar wajen tashin-tashinar da aka yi shekaru ana yi a ƙasar Hausa da sassan Kano da Hadejia? Shin mun san irin tsarin da aka gudanar na mulki a wancan zamani da irin rawar da Sarkin Bauchi Yakubu III (daga 1941 zuwa 1954) ko kuma wanda ya gaje shi daga baya, Alhaji Adamu Jumba, (daga shekarar 1955) suka wanzar a wancan lokacin?
Me ya sa ba wanda ke kawo irin takun-saƙa da aka yi tsakanin talakawa da masu mulki da hukumomin En'e da jami'an NPC da irin rawar da Lamiɗon Adamawa, Yarima Ahmadu (1946–1953) da Aliyu Musdafa (daga 1953), suka taka da harƙallar da ta faru tsakaninsu da talakawa da sauran waɗanda ba su gamsu da tsarin mulkin En'e a lokacin ba?
Wai kuwa muna da masaniyar cewa ɗarikun Ƙadiriyya da Tijjaniya, musamman a ƙasashen Kano da Sakkwato sun taka muhimmiyar rawa wajen tashin-tashinar da ta auku a Arewacin Nijeriya da zage-zage da cin mutuncin juna, har ma da kashe-kashe? Su wane ne malaman da ke da hannu a waɗannan al'amurra da suka faru? Me ya sa ɗarikar Ƙadiriyya ta zaunu a manyan ƙasashen Daular Sakkwato, aka kuma dakushe Tijjaniya? Me ya sa ɗarikar Tijjaniya ta samu gurbin zama sosai a gabashin ƙasar Sakkwato, ta mirgina ta yi tunga a sassan Kano da Zaria?
Shin wace rawa ziyarar Sheikh Ibrahim Inyass, musamman a ƙasar Kano ta taka wajen ƙara tabbatuwar ɗarikar Tijjaniya a Arewa? Shin akwai wata rubutacciyar hujja da ake da ita da ta nuna cewa Sardauna ya taɓa hana Ibrahim Inyass shiga kasar Kano ko kuma ya yi masa takunkumi da ya hana shi motsawa a tsakanin shekarun 1950 zuwa 1960 a Arewacin Nijeriya?
Za mu ci gaba