Gasar Cin Kofin Duniya: Arsene Wenger Ya Lisafta Faransa A Matsayin Wadda Za Ta Lashe kofin

Tsohon kocin kungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal, Arsene Wenger, ya bayyana ƙasar Faransa a matsayin kasar da ta fi kowace kungiya damar lashe gasar cin kofin duniya na bana.

Wenger yana da yaƙinin cewa dakarun da Didier Deschamps ke jagoranta sun taka matakin da ya fi na sauran takwarorinsu a wannan gasa.Yayin da yake zantawa da jaridar Le Figaro game da ƙasashen da ake kyautata zaton za su iya karkare gasar cikin nasara, Wenger ya bayyana cewa: "Na sanya su a gaba da sauran ƙasashen. Faransa tana da kwararrun 'yan wasa masu taron yawa, kuma Deschamps yana da kwarewar da ake bukata."

Ya kara da cewa: "Muna da 'yan wasan gaba masu yawa, wanda hakan kan iya janyo fargabar rashin samun daidaito a tsarin tsaronmu yayin da muke kai hari. Sai dai a yau, kwararren dan wasa na zamani, koda kuwa dan wasan gaba ne, ya san yadda zai bayar da nasa gudunmawar a aikin tsaron gida."

Wenger ya nuna cewa karfin jiki da karsashin 'yan wasan Faransa na zama babban makami a mintunan karshe na wasa, inda ya ce: "Idan kuna canjaras na 0-0 da Faransa yayin da ya rage mintuna 20 kacal a tashi daga wasa, to ku kaddara kun sha kashi. Karfin jiki ne ke haifar da sauyi a irin wannan lokaci."

Idan za a iya tunawa, Faransa ce ta lashe kofin duniya na shekarar 2018, sai dai ta gaza kiyaye kambunta a gasar shekarar 2022 bayan da ta sha kashi a hannun kasar Argentina a wasan karshe.

Post a Comment

Previous Post Next Post