Kafin Da Bayan Mulkin Su
Sardauna A Arewacin Nijeriya (1)
Tun da farko a sani, ni ba masanin ilimin tarihi ba ne, ɗalibi ne da ya shiga aji aka koyar da shi, yake kuma koyo har yanzu. Na matsa wa kaina yin wannan tsokaci da zai ɗauki zubi huɗu ko biyar saboda na ga ana buƙatar a buɗe wannan faifai domin ƙaruwar juna, amma duk a tsorace ake. Haka kuma ni ba ɗan siyasa ba ne, sai dai ina sha'awar harkokin siyasa domin ko ta kowace irin fuska aka dube ta, siyasa da masu gudanar da ita dole su yi tasiri a rayuwata ko ta iyalina - kai tsaye ko kaikaice; ina so ko ba na so - saboda haka janye jiki daga gare ta alamu ne na rashin sanin ciwon kai. Wani ƙarin haske kuma shi ne, ban yi wannan rubutun domin nuna in da 'yan Atiku ko Kwankwaso ko Tinubu suke da kuskure ba, ko kuma bayar da kariya ga wani sashe. Ƙoƙarina kawai in bayyana ɗan abin da na sani game da wannan zamani da kuma abubuwan da suka faru, gwargwadon iyawa, daga hujjojin da Allah ya huwace.
Fatata ita ce rubutun ya zama wata kafa ta karantar da juna da ilmantar da masu son sanin yaya ta kasance, me kuma ya sa take caɓewa a halin yanzu - tsakanin matasan da ke wannan sahar. Na yi wannan niyya ganin yadda masana da masu tattauna matsalolin tarihin Arewacin Nijeriya a yau ke gutsiri-tsoma ko yanko nan, watsar da can, ko sakin layi da gangan ko kuma a jahilce game da ainihin abin da ya faru. Ba wai ina nufin cewa dukkan abin da ake faɗa ba gaskiya ba ne, amma abin da ɗaure kai ka ji ana cewa wai Sardauna shi ne ya gina Arewa, wasu kuma na cewa ai ba abin da Sardauna ya yi sai zalunci da cin mutuncin mutane. Wasu na cewa ai Tafawa Ɓalewa ya samar da jami'ar A.B.U Zaria ba Sardaunan ba, domin ai Tafawa Ɓalewa shi ne Shugaban Nijeriya ba Sardauna ba. Wasu ma na ganin ba laifin kowa ba ne game da matsalolin Arewa sai Sardaunan, saboda shi ne ya yi mulkin kama karya, ba kowa ba.
Wasu kuma na shammato cewa wasu sarakuna suna zargin irin su Malam Aminu Kano da koya wa talakawa su ce ' 'mun ƙi' ko 'ba mu amince ba' bisa dukkan abin da masu mulki ke gudanarwa, saboda ba su da gaskiya ko munafukai ne, alhali laifin ba na Malam Aminu Kano ba ne, na Sa'adu Zungur ne - shi kuma akwai dalili, ba tsageranci ya so ya koyar ba. Wasu kuma suna jefo bayanai na kisan gilla da ɗauri da bugu da danne haƙƙi na mutane kamar a ƙasar Kano kawai aka yi waɗannan abubuwa - ga dai shibci nan na labarai da ba su da kan gado ko madafa saboda ba a fahimci tsarin shugabancin Arewa daga shekarar 1936 har zuwa 1966 da aka kashe su Sardauna da kuma rikita-rikitar da ta biyo baya ta yaƙin basasa da A-ware da makamantan su ba! Duka dai ba a samu matsaya ko madogara ɗaya ba saboda son rai, da siyasantar da lamurran.
Za mu ci gaba