Kafin Da Bayan Mulkin Su
Sardauna A Arewacin Nijeriya (2)
Daga ɗan ce-ce-ku-ce na abin da ya faru game da tarihin mulki da danniya da neman ‘yanci a Arewacin Nijeriya a ‘yan kwanakin nan sai na fahimci wani abu kuma da ya fara ba ni tsoro game da makomar matasa da sauran masu son ganin cigaban wannan yanki namu a siyasance ko addinance ko ƙabilance ko wani abu mai kama da haka!
Abin da ya fara tayar man da hankalin kuwa bai wuce ina ganin yawancin matasa ba su naƙalci abin da ya faru daga shekarar 1804 ba, lokacin kafuwar Daular Sakkwato har zuwa 1886 da Turawa suka kunno kai a Arewa zuwa 1906 da suka karɓe mulki har zuwa 1936 da aka fara nuna azama ta ƙin mulkin Turawan Ingila zuwa yau a wannan yanki namu mai matuƙar muhimmanci ga rayuwarmu ba. Idan da mun tsaya mun nazarci abubuwa da kyau tun daga 1936 zuwa yau shekara 90 ke nan na gwagwarmayar gina ƙasa da al'ummar yankin suka sa gaba da ba haka ba. A cikin wannan lokaci ne aka tabbatar da mulkin mallakar Turawa da ci gaba da gudanar da mulki daga ‘yan ƙasa bayan 'yancin kai da ɗabbaka tattalin arziki da tayar da komaɗarshi daga Turawa. Haka aka ci gaba da gungurawa da mulki ya dawo gida, waɗanda suka gaji Turawa suka ɗora, daga baya kuma tashin-tashina kala-kala da suka biyo baya a tsakanin al'ummar ba abubuwa ba ne da suke ɓoye, da mun yi nazarin su da kyau da ya taimaka da kuma mun samu ƙarin haske, mai muhimmanci.
Nakan ji gabana na faɗuwa idan na ga mutane sun manta ko kuma ba su san rawar da Sarakuna Arewacin Nijeriya suka taka ba a wannan harƙallar, ko kuma yadda talakawa suka agaza wajen rura wutar lamurran, ko kuma in ce da gangan an rufe batutuwa ne na irin rawar da Sarakuna da shugabanni da hukumomin En’e-En’e da ke mulkin Lardunan Arewa da taimakon da Alƙalai da ‘Yan Doka da ‘Yan Sanda suka bayar, da uwa-uba yadda Turawan mulkin mallaka - ciki da wajen Nijeriya suka taka muhimmiyar rawa wajen wannan tataɓurza.
Tambayar da zan fara da ita, me ya sa in ana zancen rashin adalci da cin mutuncin al'umma, musamman talakawa a wancan zamani ba a kawo sauran gungun mutane da ke da hannu kan wannan badaƙala sai a ware mutum ɗaya ko biyu daga cikin ɗaruruwa kawai, alhali kuwa akwai ƙarin wasu zube da suka taimaka, kuma bayanan nan a fili suke? Me ya sa aka fi mayar da hankali kan wasu zaɓaɓɓun matsaloli kawai ba a fasa ƙwan kowa ya ji irin warin da ke ciki, sai a fi mayar da hankali kan wane ko wance alhali kowane gida ko iyali ko jam'iyya ko yanki ko ɓangaren addini - irin su Ƙadiriyya da Tijjaniya da wasu da dama sun bayar da gudunmuwa da ta jawo badaƙalar da aka shuka a tsawon shekara 100 da suka wuce?
Za mu ci gaba