Sabbin Dokoki A Gasar Cin Kofin Duniya 2026

🚨 DA ƊUMI-ƊUMI: SABBIN DOKOKIN DA AKA TABBATAR A GASAR CIN KOFIN DUNIYA NA  2026!

1. LOKACIN JIFA (SEKON 5): Idan ɗan wasa ya jinkirta yin jifa (throwing) da gangan, za a iya ba abokan hamayya jifar.

2. ƁATA LOKACI GA GOLA YAYIN DA ƘWALLO TA FITA ( SEKON 5): Haka nan, idan gola ya ɓata lokaci da gangan wajen buga ƙwallon da ta fita, hakan na iya sa a ba da bugun kusurwa ga abokan hamayya.

3. LOKACIN CANJIN ƊAN WASA (SEKON 10): 'Yan wasan da aka canja suna da daƙiƙa 10 su fita daga fili ta wuri mafi kusa da su. Idan suka gaza yin hakan, ɗan wasan da zai shigo ba zai iya shiga fili ba na aƙalla minti ɗaya kuma ƙungiyar dole ta ci gaba da wasa da 'yan wasa 10.

4. MAGANI A WAJEN FILI (MINTI ƊAYA): 'Yan wasan da ma'aikacin lafiya ya duba dole su zauna a wajen fili na tsawon daƙiƙa 60, sai dai ban da masu tsaron raga, da kuma idan an bai wa ɗan wasan abokin hamayya katin gargaɗi ko an kore shi.

5. 'YAN WASAN DA SUKE RUFE BAKINSU: Duk ɗan wasan da ya rufe bakinsa a cikin yanayi na faɗa da abokin hamayya za a iya hukunta shi da JAN KATI (Red Card. 

6. ANA IYA DUBA BUGUN KUSURWA: VAR na iya tabbatar da cewa an bayar da bugun kusurwa daidai, amma dole ne a yi hakan cikin sauri kafin a sake fara wasa.

7. ANA IYA NAZARTAR KATI NA BIYU: 'Yan wasan da aka kora saboda karɓar katin gargaɗi biyu za a iya duba katin na biyu, amma ba za a yi nazari ba don yiwuwar katin gargaɗi na biyu. 

Post a Comment

Previous Post Next Post