Jam'iyyar NDC Ta Tsayar Da Dantakarar Gwamna A Kano

Da Ɗumi-ɗumi: Jam'iyyar adawa ta NDC a yankin Kano ta tsayar da tsohon mataimakin gwamnan Kano a jam'iyyar NNPP Kwamared Abdulsalam a matsayin ɗantakarar gwamnan Kano a gabanin zaɓen 2027, ba tare da wata hamayya ba.

Da yawan mutane sun so a ayyana tsohon ɗan takarar Gwamna na jam'iyyar APC Dakta Nasiru Yusuf Haqura, a matsayin ɗan takarar gwamnan, sai dai cikin mamaki sai aka ji an ayyana shi a matsayin ɗantakarar Sanatan Kano ta Tsakiya.

Da farko dai Gawuna ya yi turjiya tare da ƙin karɓar tayin tikitin sanatan, sai dai daga bisani kuma bayan tuntuɓa da shawarwari daga abokan siyasa sai ya amince ya karɓi takarar.

An hango wani faifan hoto mai motsi da hadin na musamman ga Kwankwaso, Saifullahi Hassan, ya wallafa, inda aka ga jagoran kwankwasiyya Dr Rabi'u Musa Kwankwaso na kira ga ɗaukacin magoya bayan siyasar Kwankwasiyya da su fito kansu da ƙwarƙwatarsu domin tabbatar da takara ta  Abdulsalam da Gawuna da kuma Peter Obi a jihar Kano a yau Juma'a.

Post a Comment

Previous Post Next Post