Manchester City Ta Yi Sabon Ango

Enzo Maresca ya sanya hannu a yarjejeniyarsa da shuwagabannin ƙungiyar Manchester City, wanda zai ci gaba da jagorantar ƙungiyar har zuwa shekarar 2029, ke nan zai shafe shekaru uku yana jagorantar ƙungiyar.

Enzo ya rattaɓa hannun jagorancin ƙungiyar ne a yau, bayan da mai horas da ƙungiyar Pep Guardiola ya yi bankwana da ƙungiyar a wasan da suka fafata na ƙarshe da ƙungiyar Aston Villa a wasan ƙarshe na gasar Premier League.

Pep Guardiola ya shafe shekaru goma cif yana jagorantar ƙungiyar, wanda a cikin waɗannan shekarun ya lashe masu manya da ƙananun kofuna har guda ashirin.

Shin kuna ganin Enzo shi ne ya fi dacewa da wannan aikin kuwa?

Post a Comment

Previous Post Next Post