Pantami Ya Samu Takarar Gwamna A Jam'iyyar PDP A Gombe Bayan Ya Rasa A APC

Tsohon ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya koma jam’iyyar PDP tare da lashe tikitin takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar.

Isa Ali Pantami

Pantami ya samu tikitin ne ta hanyar masalaha a zaɓen fidda gwani da aka gudanar ranar Talata a Gombe, inda shugaban kwamitin zaɓen PDP, Hon. Gregory Yenlong, ya bayyana shi a matsayin ɗan takara daya tilo.

Da yake jawabi bayan bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, Pantami ya ce ya shiga takarar ne domin yi wa al’ummar jihar hidima, tare da alƙawarin gudanar da mulki cikin adalci idan aka zaɓe shi a shekarar 2027.

Yanzu Pantami zai fafata da Jamilu Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar.

Kafin sauya sheƙarsa zuwa PDP, Pantami ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda APC ta zaɓi Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takarar maslaha. Ya janye daga zaɓen fidda gwani na APC ne saboda abin da ya kira rashin gaskiya da rashin bayyana gaskiya a tsarin.

Sai dai kafin zaɓen PDP, wasu masu neman takarar gwamna huɗu na jam’iyyar sun nuna adawa da shigar Pantami cikin takarar, suna masu cewa doka ba ta yarda wanda ya shiga zaɓe a wata jam’iyya ya sake shiga irin wannan tsari a wata jam’iyya ba bayan an riga an kammala zaɓe.

Post a Comment

Previous Post Next Post