Ba Bruno Ne Ya Fi Kowa Bayar Da Taimakon Ƙwallo A Gasar Premier League Ba

Hassada Ko Gaskiya?

Tsohon ɗan ƙwallon Manchester United Eric Djemba-Djemba ya bayyana cewa, ya kamata hukumar Premier League ta soke taimakon ƙwallon da Bruno Fernandez ya ba wa Patrick Dorgue a wasansu na ƙarshe (38) da Brighton a gasar cin kofin Premier League na 2025/2026.

Djemba-Djemba ya bayyana haka ne, jim kaɗan bayan ayyana Bruno a matsayin wanda ya fi kowane ɗan wasa bayar da taimakon ƙwallaye a shekara guda, wanda ya bayar da taimakon ƙwallaye 21, wanda hakan ya sa ya shafe tarihin Thiery Henry da kuma Kevin Debruyne waɗanda suke riƙe da kambun da taimakon ƙwallaye (20 kowanensu). 

Djemba-Djemba ya ce ya kamata a kashe wannan taimakon na ƙarshe, domin ƙwallon da Dorgue ya dasa mata kai, ba ta shiga taga kai tsaye ba, maimakon haka, sai da ta bugi ƙarfe sannan ta dawo ta bugi hannun hola, sannan ta shiga ragar, don haka wannan bai kamata a ƙirga shi a matsayin taimakon da Bruno ya bayar ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post