Ana Iya Daukar Shekaru Kafin Amurka Ta Mayar Da Asarar Makaman Da Ta Yi a Yakinta Da Iran

 Wani sabon rahoto ya bayyana cewa ƙasar United States na iya ɗaukar shekaru tana sake cika wasu muhimman rumbunan makamai da suka ragu bayan yaƙin da aka yi da Iran.

United States

Rahoton, wanda cibiyar bincike ta Center for Strategic and International Studies (CSIS) ta fitar, ya ce wasu manyan makamai da tsarin kariyar makamai masu linzami da aka yi amfani da su sosai a lokacin rikicin na iya ɗaukar tsakanin shekaru biyu zuwa huɗu kafin a sake samar da su yadda ya kamata, yayin da wasu ma za su iya ɗaukar lokaci fiye da haka.

Daga cikin makaman da rahoton ya ce suka fi raguwa akwai makamai masu linzami na Tomahawk, tsarin kariya na Patriot, THAAD, da kuma makaman ruwa na SM-3 da SM-6.

Masana sun bayyana cewa jinkirin sake cika rumbunan makaman na da alaƙa da ƙarancin ƙarfin masana’antu, matsalolin samar da kayan aiki, da kuma wahalar ƙera manyan makaman zamani masu fasaha.

Rahoton ya yi gargaɗi cewa wannan raguwar makamai na iya haifar wa Amurka da abin da ya kira “gibin rauni,” musamman a lokacin da ake ƙara samun tashin hankali tsakanin China da Taiwan.

Masana sun kuma ce matsalar ba wai rashin kuɗi ba ne, domin Amurka na ci gaba da kashe kuɗaɗe masu yawa kan tsaro, sai dai tsawon lokacin da ake buƙata wajen ƙera manyan makamai masu sarkakiya da fasahar zamani.

Duk da haka, jami’an gwamnatin Amurka sun ce har yanzu sojojin ƙasar na da isassun makamai domin fuskantar manyan barazana da ci gaba da ayyukansu a duniya. Sai dai masana harkokin tsaro sun bayyana cewa rikicin Iran ya nuna wasu rauni a tsarin samar da makaman Amurka na dogon lokaci.

Post a Comment

Previous Post Next Post