Kasancewar ruwan zafi abu mai muhimmaci, musamman a lokacin sanyi ko hunturu, aka ga ya dace a tattaro wasu ingantattun shawarwari domin kula da lafiyar fata da ma jiki baki ɗaya. Ga kaɗan daga cikin amfanin yin wanka da ruwan ɗumi.
Amfanin yin wanka da ruwan zafi a lokacin sanyi:
1. Yana rage jin sanyi:
Wanka da ruwan zafi yana taimakawa jikin mutum ya ji ɗumi, musamman a lokacin hunturu ko sanyi mai tsanani.
2. Yana sassauta tsokoki:
Ruwan zafi yana sa tsokoki su sake, yana rage gajiya da ciwon jiki bayan aiki ko motsa jiki.
3. Yana motsa jini:
Zafi daga ruwan wanka yana taimakawa wajen hanzarta gudun jini a jiki, wanda ke inganta lafiyar zuciya da gaɓoɓi.
4. Yana kwantar da hankali:
Wanka da ruwan zafi yana rage damuwa (stress) da tashin hankali, yana sa mutum ya ji nutsuwa.
5. Yana tsarkake fata:
Ruwan zafi yana buɗe pore ɗin fata, yana taimakawa wajen fitar da datti da mai da ke tattare da fata.
6. Yana taimakawa wajen samun barci mai kyau:
Yin wanka da ruwan zafi kafin kwanciya yana taimakawa jiki ya huta da sauƙaƙe samun bacci.
7. Yana taimaka wajen waraka daga mura ko tari:
Hucin ruwan zafi (steam) yana buɗe hanyoyin numfashi, yana taimakawa wajen rage toshewar hanci da numfashi mai wahala.
Lura: Kada ruwan ya yi zafi sosai, domin hakan na iya ƙone fata ko busar da ita. A yi amfani da ruwan dumi mai matsakaicin zafi.
