Wata rana Tabi'iy Ibrahim Ɗan Adham (100 -165 BH) ya wuce ta kasuwar Basrah, sai mutane suka yi dandazo wurinsa suna cewa: "Ya baban Is'haƙ, me yasa muna roƙon Allah, amma ba ya amsa mana?".
Sai yace: "domin zukatanku sun mutu saboda abubuwa guda goma (da kuke aikatawa)".
Sai suka ce: "waɗanne abubuwa ne?". Sai ya lissafa su kamar haka:-
1. Kuna cewa kuna son Allah, amma ba ku bada haƙƙinsa.
2. Kuna karanta Alƙur'ani, amma ba ku yin aiki da shi.
3. Kuna riya kuna son Annabi (Sallallahu alaihi Wasallam), amma kun yi watsi da sunnarsa.
4. Kun ce Shaiɗan abokin gabarku ne, amma kullum kuna biye masa.
5. Kun ce kuna son aljanna, amma ba ku yin aiki domin samun ta.
6. Kun ce kuna tsoron wuta, amma ba ku guje ma ta.
7. Kun ce mutuwa gaskiya ce, amma ba ku yi ma ta shiri (tanadi).
8. Kun shagaltu da lissafa laifukan mutane, kun manta da naku (laifukan).
9. Kuna cin ni'imar Allah, amma ba ku yin godiyar da ta dace (gare shi).
10. Kuna rufe mamatanku, amma ba ku ɗaukar izna da su.
To, ta yaya za a rinƙa karɓar addu'arku?.
Allah yasa mu gyara.
