A daren jiya Alhamis ne wasu gungun ɓarayin daji da ba a iya tantance adadinsu ba, suka kai samame a garin Ƙira da ke ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina.
Ɓarayin dajin, sun kai harin ne da dare misalin ƙarfe sha ɗaya 11:00pm na daren jiya Alhamis 09/08/2026.
Rahotommu ya ruwaito cewa, ɓarayin sun shiga garin ne, da niyyar ɗaukar wani mutum wanda ya yi hijira da daɗewa daga wani ƙauye ya koma garin Ƙira da zama, an bayyana cewa mutumin ya kai aƙalla shekaru uku da tarewa a garin Ƙira da iyalansa ya zuwa yanzu.
Ɓarayin sun samu nasarar yin garkuwa da matan aure biyu kowacce ɗauke da goyonta, sun kuma haɗa da wasu 'yan mata guda biyu. Bayan sun ɗauke su sai suka tsallaka maƙwabtan waɗannan matan suka buga gidan wani matashi, amma gidan bai buɗu ba, har ta kai ga sun harbi ƙyauren da bindiga amma duk da haka ƙyauren ya ƙi buɗewa, haka ta sa dole suka haura saman katanga, suka shiga, suka tarar da maigidan da matarsa. A nan suka yi ƙoƙarin tafiya da matar, amma mijin ya ce a'a, su ƙyale ta, shi su tafi da shi.
Haka suka tasa matashin mai suna Sulaiman Idris Wanda aka fi sani da Abbalo tare da sauran mata huɗu suka yi gaba da su.
An bayanan mana cewa, bayan sun yi nisa, har sun kai wajen wani ƙauye da ake kira 'Yarmagarya sai suka sako ƙanan matan da suka tafi da su, sannan suka umarci matan masu goyon da su ba su goyon su dawo da su gida.
Daga ƙarshe dai sun tafi da mata biyu Nafisa da Naja'atu da kuma matashi Abbalo.
Ya zuwa yanzu dai, babu wata daba da ta ɗauki alhakin kai harin, har yanzu kuma ba a kira waya domin neman kuɗin fansa ba.
Rahoton ya bayyana yadda zuwan 'yan C-Watch ya bayar da gagarumar gudummuwa, wajen ganin an taƙaita ɓarna a garin.