Wasu fusatattun mabiya Sheikh Musa Lukuwa da ke jihar Sokoto, sun yi ajalin wani matashi, wanda ya yanki malamin masu da wuƙa.
Matasan sun kashe matashin wanda ake zargi da daɓa wa wani malamin addinin Musulunci, Malam Musa Lukuwa, wuƙa jim kaɗan bayan kammala sallar Juma’a a masallacinsa da ke yankin Mabera, cikin birnin Sakkwato.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, inda rahotanni suka ce matashin, wanda ake kira da suna Mai Barewa, ya kasance cikin masu ibada a masallacin, kafin ya farmaki malamin tare da daɓa masa wuƙa har sau biyu a wuya bayan kammala sallar.
Majiyoyi sun ce masu ibadar da ke wurin sun yi nasarar cafke wanda ake zargin, inda daga bisani suka yi masa duka har ya mutu.
Rahotanni sun danganta harin da wata huɗuba da Sheikh Lukuwa ya gabatar a baya, inda ya ambaci wani Hadisi da wasu malaman addini, musamman masu alaƙa da ɗariƙar Sufaye suka ce ya ɓata sunan iyayen Annabi Muhammad (SAW).
Bayan wannan cece-ku-ce, an ce Mai Barewa ya yi barazanar kashe Malam Lukuwa da babban ɗalibinsa, Malam Murtala Assada.
Malamin da mabiyansa sun kai rahoton barazanar ga ’yan sanda, lamarin da ya kai ga kama matashin da kuma gurfanar da shi a gaban kotu. Wanda daga ƙarshe kotun ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali na wani lokaci, yayin da shari’ar ke ci gaba.
Kwanaki huɗu kafin harin na yau Juma’a, Malaman sun kuma ziyarci fadar gwamnatin jihar Sakkwato, inda suka gabatar da rubutaccen ƙorafi kan lamarin, bayan haka ma, an hango Malam Musa Assada a wani faifan bidiyo yana jaddada dukkan abubuwan da suke faruwa, tare da ƙara jaddada kai kukansu ga gwamnati domin ɗaukar matakin Shari'a.
Da yake tabbatar da faruwar harin, kakakin rundunar ’yansandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce, Malam Lukuwa na nan da ransa, sai dai yanzu haka yana karɓar magani a Asibitin Ƙwararru na Sokoto.
Ya ƙara da cewa mabiyan malamin ne suka kashe wanda ake zargin bayan sun cafke shi a hannu.
Kakakin ’yansandan ya ƙara da cewa kawo yanzu ba a kama wani mutum dangane da tashin hankalin ba, sai dai rundunar ta ɗauki matakan da suka dace domin hana lamarin ƙara ta’azzara.
Ahmad ya ƙara da cewa ’yansanda na gudanar da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa harin da kuma gano duk mutanen da ka iya kasancewa da hannu a lamarin.