Hassada mugun ciwo, bayan kammala naɗin Bello Usman a matsayin sabon ma'ajin ƙaramar hukumar Musawa. Wasu 'yan hassada da suka fito daga cikin ma’aikatan Karamar Hukumar ta Musawa a Jihar Katsina sun nuna hassada da takaici gami da ƙorafinsu a fili kan yadda aka ce an tura wani ma’aikaci da ba shi da ilimi, a kan harkokin kuɗi domin ya zama Ma’aji na ƙaramar hukumar.
Wani jigo a ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi daga Musawa, wanda ya nemi a sakaya sunansa a wata ziyarar bazata da suka kai a gidan jaridar Katsina Times, ya jagoranci wasu daga cikin ma’aikata 'yan'uwansa, inda suka bayyana ƙorafinsu.
Ma’aikatan sun ce mutumin da aka naɗa, mai suna Bello Usman, yana da digiri a fannin Ilimin Mulki, wanda suka ce ba fannin harkokin kuɗi ba ne. Sai dai sun manta, ba su bayyana wane irin aiki Bello Usman yake yi a ƙaramar hukumar ba na tsawon lokaci.
Bello Usman, a yanzu haka Senior Accountant ne na ma'aikatar a sashen kuɗi ta ƙaramar hukumar, wanda yake aiki a ma'aikatar tun shekarun 1995. Sai dai ciwon hassada ya kasa sa su gane bai cancanta ba, tun a wancan lokacin sai yanzu da wannan ci gaban ya tunkaro shi.
Bayan duka waɗannan bayanan, kafin a ba wa Bello wannan matsayi, sai da hukuma ta tantance shi sannan ta yi duk irin bincikenta ta ga dacewarsa sannan ta ba shi wannan matsayi, amma kai tsaye wani maƙiyin ƙaramar hukumar Musawa, maƙiyin gwamnatimmu ta APC ya zo yana sukar waɗanda suka yi wannan aiki. Wannan aiki ne na rashin ɗa'a kuma muna tir da Allah wadai da shi.
Sun ce sun gabatar wa da jaridar Katsina Times wasu hujjoji da suka shafi takardun karatu da ƙwarewar wanda aka naɗa. A cewarsu, akwai ƙwararrun ma’aikata a Sashen Kuɗi na Karamar Hukumar Musawa waɗanda suke da digiri da sauran ƙwarewa a fannin harkokin kuɗi, tare da gogewar aiki.
“Idan za a gudanar da jarabawa kan wannan fanni, akwai ma’aikatan da suka ƙware sosai kuma suka dace da wannan matsayi,” in ji ɗaya daga cikin ma’aikatan. Sai dai duk da sun san da waɗannan gogaggun mutanen amma ba su iya bijirar da su ba, sai da batun naɗin sabon ma'aji ya taso.
Har wa yau, sun yi zargin cewa an tsallake irin waɗannan ma’aikata, aka naɗa wani da suka ce ya fito daga wani fanni daban domin ya zama Ma’aji na karamar hukumar. Ma’aikatan sun kuma yi zargin cewa sabon wanda aka ba matsayin yana fuskantar ƙalubale wajen gudanar da wasu ayyukan da suka shafi muƙaminsa, inda suka ce wasu ayyukan sun tsaya saboda yana ƙoƙarin fahimtar yadda ake gudanar da aikin.
A cewarsu, wannan mataki ya saɓa da tsarin cancanta da ƙwarewa da suke ganin gwamnatin Gwamnan Jihar Katsina ke ƙoƙarin tabbatarwa.
Sun roƙi Gwamnan Jihar Katsina da ya sa a binciki lamarin tare da ɗaukar matakin da ya dace.
Wannan ne ya sa, mutanen suke ta yawo lungu da saƙo, duk inda suke ganin suna da uwa a gindin murhu, suna kai ƙarar lamarin domin ganin an tunɓuke sabon Ma'ajin kawai saboda wani dalili na ƙashin kai.
Maziyartan sun kara da cewa, “Ya kamata a bai wa waɗanda suka ƙware kuma suka karanci harkar kuɗi damar gudanar da aikin, yayin da shi kuma a ba shi matsayin da ya dace da fannin da ya karanta.”
Sun ce ɗaukar irin wannan mataki zai tabbatar da adalci a Karamar Hukumar Musawa tare da inganta gudanar da ayyukanta. Ma’aikatan sun kuma bayyana cewa akwai rashin jin daɗi da damuwa a tsakanin wasu ma’aikata kan wannan mataki, wanda suka ce zai iya yin tasiri ga yadda ake gudanar da ayyuka, tare da yiwuwar haifar da tasiri a harkokin siyasar yankin.
Jaridar Katsina Times ta yi ƙoƙarin jin ta bakin shugaban Karamar Hukumar Musawa kan zargin, amma bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba. Haka kuma, an tura masa saƙon rubutu, amma har zuwa lokacin kammala wannan rahoto bai bayar da amsa ba.
Jaridar ta kuma tuntuɓi kakakin Hukumar Kula da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Jihar Katsina, Alhaji Bishir, wanda ya ce bai da masaniya kan wannan zargi.
Sai dai ya shawarci duk wani ma’aikaci da ke da ƙorafi kan wani ma’aikacin da aka tura masa wajen aiki da ya rubuta ƙorafinsa a hukumance.
Ya ce idan aka gabatar da korafin ta hanyar da ta dace, hukumomin da abin ya shafa za su saurari masu ƙorafin tare da duba lamarin.
Sai dai ya zuwa yanzu da muke kammala rahoton nan, ba mu samu wani rubutaccen ƙorafi daga ma'aikatan ba.