Hukumar 'Yansandan Nijeriya Sun Kori Jami’ai Uku Bisa Zargin Kashe Wani Matashi a Jihar Rivers, Yayin da Ake Ci Gaba Da Neman Daya Ruwa a Jallo

Rundunar 'yansandan Jihar Rivers ta kori wasu jami’anta guda uku da ake zargi da hannu wajen harbin wani mazaunin Port Harcourt, Anthony Obodo, wanda rahotanni suka bayyana cewa ɗalibi ne da ya kammala karatu a Jami’ar Port Harcourt (UNIPORT).

Kwamishinan ’yansandan jihar, Olugbenga Adepoju, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Port Harcourt, yayin da ya gabatar da jami’an da lamarin ya shafa.

Adepoju ya ce lamarin ya faru ne a ranar 27 ga Agusta, 2026, lokacin da wata tawagar ’yansanda daga sashen Agip ke dawowa daga aikin tsaro a filin wasa na Yakubu Gowon.

A cewarsa, jami’an sun hango wata mota ƙirar Lexus mai baƙin launi wadda gilashinta suke a rufe, inda suka yi ƙoƙarin tsayar da ita, amma direban ya ƙi tsayawa, lamarin da ya sa jami’an suka bi motar a baya.

Kwamishinan ya ce a yayin bin motar, wani ɗan sanda mai muƙamin corporal, Alfred Louis, ya yi harbi da bindiga wanda ya sami direban.

An garzaya da Obodo zuwa asibitin Palmars da ke Port Harcourt domin ceto ransa, sai dai abin ya ci tura, domin likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Kwamishinan ya ce an kama jami’an tawagar tare da tsare su a sashen binciken manyan laifuka na jihar (CID), inda aka gudanar da cikakken bincike.

Ya ce an kuma fara neman wani jami’in ’yansanda, Inspector Solomon Nwogu, wanda ake zargi da guduwa bayan faruwar lamarin.

Adepoju ya ce bayan kammala bincike da tabbatar da hannu jami’an a lamarin, an gurfanar da su a gaban kwamitin ladabtarwa na cikin gida, wanda ya ba da shawarar korarsu daga aikin ɗansanda.

Sufeta ya ƙara da cewa za a gurfanar da jami’an a gaban kotu domin fuskantar tuhume-tuhumen laifi da suka dace da doka.

Post a Comment

Previous Post Next Post