Kuwait Na Ci Gaba Da Dakile Hare-hare Daga Iran

Sa’a guda bayan da sojojin Kuwait suka sanar da cewa tsarin kariyar sararin samaniyar ƙasar na daƙile hare-haren makamai masu linzami da jiragen sama mara sa matuƙa da suka fito daga Iran, kamfanin dillancin labarai na Tasnim, mai alaƙa da Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC), ya bayar da rahoton cewa sansanonin sojin Amurka da ke Kuwait sun fuskanci hare-haren Iran.

Tasnim ta ce an kai hare-haren ne da makamai masu linzami da jiragen sama mara sa matuƙa, sai dai kamfanin bai bayar da ƙarin cikakkun bayanai kan wuraren da aka kai harin ko irin ɓarnar da aka samu ba sakamakon harin.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, cibiyar da ke lura da ayyukan sojojin Amurka ba ta fitar da wata sanarwa da ta tabbatar ko musanta rahoton ba.

Tsauraran matakan taƙaita yaɗa bayanai da ake gani a wasu ƙasashen yankin Tekun Fasha na ƙara wahalar da kafafen yaɗa labarai wajen samun damar shiga kai tsaye wuraren da ake zargin an kai hare-haren.

Haka kuma, Amurka ta sanya wasu matakai na sa-ido kan yadda ake wallafa hotunan tauraron ɗan adam da suka shafi sansanonin sojojinta a yankin.

A ranar Laraba, Tasnim ta wallafa wasu hotunan sama da ta ce an ɗauko ne bayan hare-haren da Iran ta kai ranar Talata kan sansanonin Amurka da ke Jordan. Kamfanin ya yi iƙirarin cewa hotunan na nuna ɓarnar da hare-haren suka haifar, sai dai ba a samu wani tabbaci mai zaman kansa kan waɗannan zantukan ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post