Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Naira Biliyan 10 na TETFund

Gwamnatin Tarayya ta amince da ware naira biliyan 10 domin tallafa wa zagayen bayar da tallafin bincike na shekarar 2026, ƙarƙashin Asusun Bincike na Ƙasa (NRF) na Asusun Amintaccen Ilimin Manyan Makarantu (TETFund).

Tertiary Education Trust Fund (TETFund)

Adadin ya nuna ƙarin kashi 64.2 cikin 100 idan aka kwatanta da naira biliyan 6.09 da aka ware domin ayyukan bincike 174 a zagayen tallafin shekarar 2025.

TETFund ce ta bayyana hakan a cikin sanarwar neman taƙaitattun bayanan ayyukan bincike (Concept Notes) na zagayen tallafin NRF na shekarar 2026, wadda Sakataren Zartarwar Asusun, Arch. Sonny Echono, ya sanya wa hannu.

A cewar Echono, ƙarin tallafin na da nufin ƙarfafa bincike da bunƙasa ƙwarewar masu bincike na Najeriya.

Asusun ya sanar da cewa za a buɗe shafin yanar gizon neman tallafin domin karɓar taƙaitattun bayanan ayyukan bincike daga 31 ga Agusta, 2026, yayin da wa'adin ƙarshe na gabatar da su zai kasance 15 ga Oktoba, 2026.

TETFund ta ce za a yi amfani da naira biliyan 10 ɗin wajen tallafa wa bincike a fannoni 30 da aka sanya wa fifiko, waɗanda suka haɗa da Nazarin Ɗan Adam da Kimiyyar Zamantakewa; Kimiyya, Injiniyanci, Fasaha da Ƙirƙire-ƙirƙire; da kuma sauran fannoni masu alaƙa da juna.

A cewar Asusun, matakin farko na neman tallafin shi ne gabatar da taƙaitaccen bayanin aikin bincike daga Babban Mai Bincike (Principal Investigator – PI). Sai dai masu neman tallafin da aka tantance ayyukansu kuma aka tabbatar za su iya samun tallafi ne kawai za a gayyace su su gabatar da cikakken shirin binciken.

Asusun ya ce malaman manyan makarantun gwamnati a Najeriya ne suka cancanci neman tallafin, yayin da za a ƙarfafa binciken da ya haɗa masana daga fannoni daban-daban.

TETFund ta ƙara da cewa dole ne Babban Mai Binciken ya kasance ma'aikacin wata cibiya, kuma cibiyar da yake aiki a cikinta za ta kasance cibiyar kula da aikin binciken, tare da ɗaukar alhakin tabbatar da yadda ake amfani da kuɗin tallafin.

Asusun ya bayyana cewa bayan kammala tantancewa, za a gabatar da ayyukan binciken da suka yi nasara ga Kwamitin Amintattu na TETFund domin amincewa da bayar da kuɗaɗen tallafin.

TETFund ya ce za a gudanar da dukkan tsarin neman tallafin ne ta yanar gizo, ta hanyar shafin yanar gizon Asusun Bincike na Ƙasa (NRF).

Ya kuma jaddada cewa za a tantance dukkan takaitattun bayanan ayyukan binciken da aka gabatar ta hannun Kwamitin Tantancewa da Sa-Ido na Asusun Bincike na Ƙasa (NRFS&MC).

Bayan haka, za a gayyaci waɗanda suka yi nasara domin su ƙara bayani tare da gabatar da cikakken shirin bincikensu.

Asusun ya ce Babban Mai Binciken da kuma aƙalla mutum ɗaya daga cikin ƙungiyar masu gudanar da binciken za su fuskanci kwamitin domin kare tare da bayyana muhimmancin ayyukan binciken kafin a amince da tallafin.

Post a Comment

Previous Post Next Post