Arsenal Ta Fara Kakar Wasannin 2026/2027 Da Kafar Dama, Bayan Da Ta Doke Manchester City Da Ci 3 Da 0 a Wasan Community Shield (Charity Cup)

Tawagar 'yan wasan Arsenal sun lallasa ƙungiyar Manchester City da ci 3 da nema 0 a wasan cin kofin Charity Cup.

Inda a wasan, sabon ɗan wasan gefen na Arsenal Ricardo Calafiori ya fara zura ƙwallo a cikin sakanni 25 da fara wasan. Sai kuma Kai Hervertz da ya saka ƙwallo ta biyu a mintina na 28 yayin da ɗan wasan tsakiyar ƙungiyar Martin Ordegard ya zura ƙwallo ta 3 a mintina na 48 kuma ta ƙarshe a gasar.

Gasar Charity Cup wani faranti da ake sa ran duk ƙungiyar da ta yi nasara za ta lashe shi. Ƙungiyoyin da suka lashe kofin Premier League na Ingila da takwarata wadda ta lashe kofin F.A Cup da ake bugawa a Ingilar ne suka haɗuwa su kece raini domin ɗaukar farantin.

A wasan da ya gudana da ƙarfe 3 na ranar Lahadi, Arsenal ta koyawa Manchester City ƙwallo a filin wasan, tare da zuga masu ruwan ƙwallaye har uku ba ko ɗaya a raga, wanda hakan ya ba ƙungiyar ta Arsenal damar yin awon gaba da farantin a matsayin nasararsu ta farko a sabuwar kakar wasanni ta 2026/2027.

Shin kuna ganin wannan nasarar za ta ɗore?', duba da yadda suka fito da ƙarfinsu a wasan na jiya? Ko dai kuma ganin sun ci taliyar ƙarshe?

Post a Comment

Previous Post Next Post