Kalaman ɗan takarar gwamnan jihar Gombe na jam'iyyar PDP Farfesa Isah Ali Pantami ke nan bayan samun nasarar Maryam a gasar Ƙur'ani ta mata ta duniya.
Muna farin cikin taya 'yarmu, Malama Maryam Ibrahim Ɗan’azumi daga Jihar Gombe, da malamanta, iyayenta, da kuma 'yan'uwanta ɗalibai murna bisa gagarumar nasarar da ta samu a Gasar Ƙur'ani ta Duniya karo na 46 da aka gudanar a Makka, Masarautar Saudiiyya, inda ta zo ta ɗaya a ɓangaren Mata na Hizbi 60 da kuma Tafsiri.
Wannan babbar nasara ce ga Maryam, iyalinta, da kuma dukkan ɗaliban ilimi. Nasararta a matakin ƙasa da ƙasa ta kawo mana farin ciki da gagarumin alfahari.
Maryam ƙanwa ce ga Malama Hajara Ibrahim Ɗan'azumi, wadda ita ma ta sa Nijeriya alfahari a shekarar 2024 ta hanyar zamowa zakara gabaɗaya a Gasar Kur'ani ta Duniya ta Mata karo na 18 da aka yi a kasar Urdun (Jordan). Biyo bayan wannan nasara, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ba Hajara kyautar mota ta musamman tare da ba ta gurbin karatu (scholarship) domin ɗaukar nauyin karatunta har zuwa kammala jami'a, wanda ya biya kuɗin gabaɗaya a tsaye tun a shekarar 2024.
Farfesa Isa Ali Pantami ya daɗe yana ba fannin ilimi da gina matasa muhimmanci ƙwarai da aniya. Ya yi amanna cewa idan aka ba matasa dama da ƙwarin gwiwar da suka dace, za su iya samun manyan nasarori tare da kawo wa iyayensu, da al'ummarsu, da ƙasarsu mutunci.
Bugu da ƙari, ganin 'yan'uwa mata biyu suna samun gagarumar nasara a gasannin Kur'ani na duniya abin faranta rai ne ƙwarai da gaske.
Nasarar Maryam abin alfahari ce ga iyalinta, sannan kuma tana nuna irin hazaƙa da damar da matasan Jihar Gombe musamman, da Nijeriya bakiɗaya ke da ita.
An kammala taron karo na 46 na Gasar Kur'ani Mai Girma ta Duniya ta Sarki Abdulaziz ta haddar Ƙur'ani da Karatu, da kuma Fassarar Al-ƙur'ani Mai Girma (Tafsir) a Makka ƙarƙashin kulawar Mai Kula da Masallatai Biyu Masu Tsarki, Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud. Wadda Ma'aikatar Sha'anin Musulunci da Da'awa na ƙasar suka shirya, gasar ta samu halartar mutane maza da mata guda 334 daga ƙasashe 133, wanda shi ne adadi mafi yawa na mahalarta a tarihin gasar.
Muna miƙa godiyarmu ga Masarautar Saudiiyya, ƙarƙashin jagorancin Mai Kula da Masallatai Biyu Masu Tsarki, Sarki Salman bin Abdulaziz, da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, bisa kyauta ta musamman ta Riyal na Saudiiyya dubu ɗari uku (300,000 Riyals) wanda ya kai kusan Naira miliyan 120 da aka ba Maryam.
Allah Ya ƙara wa Maryam da Hajara ilimi, Ya albarkaci ƙoƙarinsu, sannan ya ci gaba da yi musu jagora. Allah ya sanya Ƙur'ani ya zamo haske da albarka a rayuwarsu, kuma ya ba su da sauran ɗaliban ilimi a Nijeriya da ma duniya bakiɗaya nasarori masu ɗimbin yawa.