An Tsare Tsohon Zakaran Wasannin Commonwealth a Morocco Kan Laifin Cin Zarafin Ƙaramin Yaro

Tsohon zakaran tseren mita 200 na Wasannin Commonwealth, Leon Baptiste, mai shekaru 41, yana zaman gidan yari a Morocco bayan da wata kotu ta same shi da laifin da ya shafi cin zarafin wani ƙaramin yaro ta hanyar lalata.

An bayyana cewa an tsare Baptiste a birnin Marrakech tun watan Mayun 2026, inda daga bisani aka same shi da laifi tare da yanke masa hukuncin ɗaurin watanni 10 a gidan yarin Al-Oudaya.

Wata majiya daga Ma’aikatar Shari’a ta Morocco ta tabbatar da wa BBC cewa Baptiste bai ɓace ba kamar yadda rahotanni suka bayyana a baya. Ta ce yana cikin koshin lafiya kuma bai taɓa yanke hulɗa da muhallinsa ba.

Hukumar Masu Gabatar da Ƙara ta Morocco ita ma ta tabbatar da tsare shi, tana mai cewa ɗan ƙasar Birtaniya yana zaman gidan yari a Marrakech ne bisa hukuncin kotu da aka yanke masa dangane da wani laifi.

Ya daina hulɗa da ’yan wasan da yake horaswa

Baptiste ya daina sadarwa da ’yan wasan da yake horaswa sama da watanni uku da suka gabata, lamarin da ya sa ’yan wasan da hukumar UK Athletics kasa sanin inda yake.

A watan Mayu, rahotanni sun ce ya aika wa ’yan wasan da yake horaswa da gajeren saƙo yana sanar da su cewa zai ɗan janye daga atisaye “na wani lokaci”, ba tare da bayyana dalilin hakan ba.

A lokacin, ’yan wasan na shirin shiga manyan gasa, ciki har da Wasannin Commonwealth da Gasar Turai, ba tare da jagorancin kocinsu ba.

Baptiste ya kasance mai ba da shawara kan horar da ’yan tseren gudu ga UK Athletics, inda yake horas da wasu fitattun ’yan wasan Birtaniya. A shekarar 2023 kuma an zaɓe shi a matsayin Kocin Shekara na England Athletics a lambar yabo ta Sporting Equals Awards.

Rahotannin ƙarshen mako sun bayyana cewa Baptiste ya ɓace ne a Morocco, amma daga baya aka gano cewa ya je Marrakech tare da wasu tsofaffin ’yan wasan Birtaniya uku, waɗanda duk suka koma Birtaniya daga baya.

Birtaniya ta tabbatar da taimaka masa

Ma’aikatar Harkokin Wajen Birtaniya ta tabbatar da cewa gwamnati na ba Baptiste tallafin jakadanci.

Wani kakakin ma’aikatar ya ce gwamnati na tallafa wa wani ɗan ƙasar Birtaniya da ake tsare da shi a Morocco, tare da ci gaba da tuntuɓar hukumomin ƙasar.

An kuma fahimci cewa iyalan Baptiste sun san da zaman da yake yi a gidan yari.

A ranar Talata kuma, an aika wa ’yan wasan da yake horaswa da saƙon imel na murabus daga aikinsa. Saƙon ya danganta murabus ɗin da wasu matsalolin lafiya da ba a fayyace ba, ba tare da ambaton hukuncin da aka yanke masa ko zaman gidan yari ba.

Baptiste ya lashe lambar zinare ta mita 200 a madadin Ingila a Wasannin Commonwealth na shekarar 2010. A lokacin da yake fafatawa, ya fi mayar da hankali kan tseren mita 100 da 200, kafin daga bisani ya koma aikin horas da ’yan wasa a fagen wasannin guje-guje na Birtaniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post