Mambobin kwamitin zartarwa na Ƙungiyar ’Yan Kasuwa, Masana’antu, Ma’adinai da Aikin Gona ta Jihar Zamfara (ZACCIMA), tare da wakilan ƙungiyoyin ’yan kasuwa sama da 30 a jihar, sun amince baki ɗaya da ƙuri’ar rashin amincewa da Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Farko, Chika Galadima, bisa zargin aikata wasu kura-kurai.
A cewar mambobin, an tsige Galadima ne bisa ƙudirin bai ɗaya da kwamitin zartarwa da shugabannin ƙungiyoyin ’yan kasuwa suka cimma a taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyar da aka gudanar a Otal ɗin Falala da ke Gusau ranar Laraba, 19 ga Agusta, 2026.
Mambobin kwamitin sun shaida wa manema labarai cewa an cire Galadima daga mukaminsa ne saboda wasu laifuka da suka haɗa da jinkirin ɗaukar matakan da za su bunƙasa tare da ciyar da ƙungiyar gaba, da kuma mayar da harkokin ƙungiyar tamkar na kansa, da sauran laifuka makamantansu.
Kwamitin ya kuma amince baki ɗaya da naɗa Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Biyu, Alhaji Abubakar Kabir, domin ya maye gurbin Chika Galadima a matsayin Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Farko.
Mambobin kwamitin da ’yan kasuwar sun bayyana cewa sun tsige Galadima ne saboda laifuka daban-daban, da kuma gazawarsa wajen jagorantar ƙungiyar bisa hanyar da ta dace.
A nasa jawabin bayan karɓar sabon mukamin, sabon Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Farko, Alhaji Abubakar Kabir, ya gode wa mambobin kwamitin zartarwa da kuma wakilan ƙungiyoyin ’yan kasuwa na jihar bisa amincewa da naɗa shi.
Ya ce ya amince da naɗin, tare da alƙawarin yin aiki kafada da kafada da dukkan masu ruwa da tsaki domin bunƙasa harkokin kasuwanci a Jihar Zamfara.