Wani Matashi Mai Shekaru 19 Daga Jihar Katsina Ya Zama Zakaran Gwajin Dafi Wajen Kera Mota Mai Amfani da Wutar Lantarki

Wata fasaha ta wani matashi ɗan asalin ƙaramar hukumar Kusada da ke Jihar Katsina, Ishaƙ Jamilu Kusada, mai shekaru 19, ta ɗauki hankalin al'umma da masu sha’awar fasahar ƙera motoci, sakamakon bajintarsa wajen samar da tsarin mota mai amfani da wutar lantarki kuma mai sauƙin kuɗi.

Matashin ya fara bayyana sha’awar ƙera motoci na zamani tun yana ƙaraminsa. Kafin daga bisani ya fara amfani da dabarar nan ta koyi da kanka, inda ya fara koyon dabarun Automotive Design ta hanyar amfani da intanet, da zane-zane da kuma fasahar ƙirar abubuwa ta kwamfuta ta 3D modelling.

Ishaƙ ya ɗan samu tasgaro saboda rashin samun cikakken horo daga jami'a a fannin, amma duk da matashin ya samu damar haɓaka basirarsa har ya samar da ƙira mai ɗauke da salo na zamani wadda aka tsara bisa manufar rage kuɗin samar da motocin lantarki.

Jaridar 365 ART+ Magazine ta bayyana cewa, sabuwar ƙirar motar lantarkin da Ishaƙ ya sanar, ta samu cikakkiyar kulawa, ta kuma bayyana manufar samar da motocin lantarki masu araha ba tare da rage ingancin aiki ko amfani da fasahar zamani ba.

Fasalin ƙirƙirar tsarin motar ya ƙunshi ƙaramin jiki mai amfani da sarari yadda ya kamata, tare da tsarin cikin gida da aka tsara domin sauƙin amfani da kuma ingantaccen amfani da makamashi.

Jaridar ta wallafa cewa, baya ga ƙirƙirar motoci, Ishaƙ yana da fasaha wajen gyaran motocin zamani. Wadda wannan ƙwarewar ce ta ba shi damar fahimtar yadda abubuwan da yake ƙerawa za su iya yin aiki a zahiri.

Jaridar ta ce, ɗaya daga cikin ayyukan matashin mafi shahara shi ne yadda ya gyara tare da sauya fasalin wata mota ƙirar  Peugeot 406 Sedan, inda ya yi amfani da basirarsa wajen sauya mata da sabon salo.

A cewar bayanan da aka wallafa game da aikinsa, Ishaƙ Jamilu Kusada yana neman ƙarin horo da ilimi a fannin ƙera motoci domin faɗaɗa ilimi da kuma ƙwarewarsa. Manufarsa ita ce ci gaba da aiki kan dabarun samar da motoci Masu amfani da lantarki kuma masu sauƙin mallaka, tare da rage tsadar samarwa ba tare da yin illa ga inganci ko kuma yanayin aiki motocin ba.

Lallai ƙoƙarin matashin ya ƙara fito da irin rawar da matasa za su iya takawa wajen ƙere-ƙeren kayan zamani, idan har aka ba su damar koyon sana'o'in zamani da bunƙasa basirarsu.

A lokacin da duniya ke ƙara mayar da hankali kan motoci Masu aiki da wutar lantarki da hanyoyin sufuri masu amfani da makamashi yadda ya kamata, irin wannan yunƙuri daga matashi ɗan Nijeriya na iya zama wata hanya ta ƙarfafa matasa su shiga fannin fasaha da ƙere-ƙere.

Wannan labarin ba wai na ƙirar mota ba ne kawai, labari ne na bayyana ƙwazo da jajircewa, gani da  koyon sana'a da ƙoƙarin matasa wajen mayar da tunaninsu zuwa abin da zai iya amfanar kansu da ma al'umma bakiɗaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post