Da safiyar yau Alhamis 13/08/2026 da misalin ƙarfe sha ɗaya na safe, ɓarayin daji suka kutsa ƙauyen Fulalawa da ke ƙaramar hukumar Musawa ta jihar Katsina inda suka yi harbe-harbe.
Mun samu rahoton shigar ɓarayin daji garin Fulalawa inda suka yi harbe-harben kan mai uwa da wabi, wanda hakan ya tilastawa mazauna yankin shigewa cikin gidajensu. Faruwar hakan ke da wuya sai suka fara shiga shagunan masu caji suna satar wayoyi da kuɗaɗe.
Jim kaɗan bayan faruwar al'amarin jami'an C-Watch da na 'yansandan ƙaramar hukumar Musawa suka samu rahoto, wanda hakan ya sa suka yi azama wajen kai agaji. Rahoton ya bayyana cewa, an daɗe ana ba ta kashi tsakanin jami'an tsaro da ɓarayin dajin.
Sai dai, daga ƙarshe, jami'an tsaron sun yi ƙoƙarin fatattakar ɓarayin dajin inda suka harbi mutum ɗaya daga cikin ɓarayin, tare da ƙwace sabbin babura guda biyu.
Jami'an sun kuma yi nasarar ƙwace wani babur ƙirar roba-roba na wani mazaunin garin Marabar Musawa da ake kira da Ɗan Turai, tare da amshe buhu guda da suka cika da wayoyin mutane da kuɗaɗe. Baya ga nan ma sun daƙile tare da hana ɓarayin tafiya da dabbobi da suka sata kimanin guda 120; shanu sittin (60) da kuma tumakai sittin (60).
Al'ummar Garin Fulalawa sun yi matuƙar farin ciki gani da nuna kin daɗinsu a kan wannan nasara da jami'an tsaro suka samu a kan waɗannan ɓarayi.