Shugaban 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane, Kachalla Muhammadu wanda ya fi shahara da Maha, ɗan ta'addan da ya yi garkuwa da tsohon janaral na soja marigayi (Major Janaral Rabe Abubakar) har ya ga bayansa, ya san ƙauyen Guru da ke gundumar Sukuntuni ƙaramar hukumar Kankia ta jihar Katsina gaba.
A wata fira da ɗanɗan mai garin Sukuntuni ya yi da gidan talabijin na JBC ya bayyana cewa, ba tun yanzu Kachalla Maha Ya ɗora masu ƙahon zuƙa ba, domin ya daɗe yana zuwa garin ya ci karensa babu babbaka, ya shigo lokacin da yake so kuma ya fita lokacin da yake so, ba tare da ya samu wata turijiya daga al'ummar gari ko hukuma ba.
A baya-bayan nan dai an samu wani yunƙuri da al'ummar garin suka yi, lokacin da shi Mahada yaransa suka shigo ƙauyan nasu, ganin cin kashin ya yi yawa, ya sa suka yi kukan kura a kansa wanda hakan ya sa Allah ya taimake su, suka samu nasarar hallaka masa yaro guda tare da fatattakarsu suka bar ƙauyan a lokacin.
Faruwar wannan al'amari ya sa suka yi ƙoƙarin sanar da mahukunta wanda daga ciki har da shugaban ƙaramar hukumar Kankia amma dai har yau ɗin nan ba wani mataki da aka ɗauka.
Bayan illar da suka yi wa Maha, sai ya dawo ya ƙaƙaba masu haraji na Naira Miliyan Biyar wanda ya ce za su biya shi a cikin mako guda. Mutanen nan ba wata sana'ar kirki suke yi ba, ga shi kuma abin da suka dogara da shi noma da kiwo ya bi duk ya dace dabbobin ga ya ake tunanin su samar da waɗannan kuɗaɗen wannan ne fa ya sa wasu suka yi yin ƙaura domin su tsira da rayuwarsu.
A haka Maha ya ci gaba da kai farmaki yana kashe mutane a cikin gonakinsu. Daga baya kuma ya shiga gari ranar Asabar ya kashe mutane biyu. Rashin ɗaukar wani mataki ya sa washegari ranar Lahadi ya sake komawa ya bindige mutane bakwai har lahira tare da ƙone gidaje bakwai duk don ba su biya kuɗin fansar da ya ɗora masu ba.
Bai tsaya nan ba, ranar Litinin ma ya sake komawa ya kashe mutane biyar (5), waɗanda aka haɗa za aka ga a jumlace ya kashe mutane goma sha huɗu (14) a cikin kwana 3 a jere ba tare kuma da gwamnati ta ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki ba.
Mai maganar ya yi kira ga gwamnati da ta dubi Allah ta tuna yankin Sukuntuni fa su ta zaɓa ya kamata kuma su kawo masu ɗauki kamar yadda suke kai wa kowace al'umma. Ya yi roƙo da a kai masu jami'an tsaro a yankin domin tun daga Rimaye har ɓullar wannan hanyar zuwa Soro Ɗaya babu jami'in tsaro na ɗansada ko C-Watch ko soja ko guda ɗaya duk da barazanar rasa rayukansu da suke a ciki kullum. Sannan ya yi kira da a taimake su da motar nan da ake kira APC wato mota mai sulke a yankin.