Rahotanni sun ce aƙalla mutum 37 ne suka mutu bayan sun shaƙi hayaƙi mai guba a yayin da ake zarginsu da satar man fetur daga wani bututun mai a kudancin Najeriya.
Wata ƙungiyar kare muhalli ta yankin ta ce lamarin ya faru ne a wani wurin sauke kaya da jiragen ruwa ke amfani da shi (jetty) a Jihar Ribas, a daidai lokacin da ake tura man fetur.Bayanai sun ce har yanzu akwai wasu mutane da ba a san inda suke ba.
Ƴan sanda sun tabbatar da cewa an samu asarar rayuka sakamakon lamarin, amma sun ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka mutu ko waɗanda abin ya shafa ba.