A wani gagarumin yunƙuri na bayar da gudummawa wajen bunƙasa ilimi da harkokin kiwon lafiya, Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya ƙaddamar da Ibrahim Kabir Masari Medical Students Scholarship (IKMSS) domin tallafa wa ɗaliban Jihar Katsina da ke karatun fannonin likitanci da sauran fannoni masu alaƙa da harkokin kiwon lafiya.
An samar da wannan tallafin karatu ne domin bai wa ɗaliban Katsina masu karatun likitanci da sauran fannoni masu alaƙa da kiwon lafiya a jami'o'in Nijeriya da aka amince da su tallafi da ƙarfafawa wajen ci gaba da karatunsu.
A ƙarƙashin shirin an sanar da sabuwar manhajar, wanda ya ce, ta wannan muhimmiyar manhaja, Alhaji Ibrahim Kabir Masari na da burin bayar da gudunmawa wajen samar da sabbin ƙwararrun ma'aikatan lafiya da za su taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ayyukan kiwon lafiya da inganta rayuwar al'umma.
Mai ba wa Smshugaban ƙasar shawara a fannin siyasa ya bayyana fannonin da tallafin zai fi shafa kai tsaye da suka haɗa da:
Medicine and Surgery (MBBS) da Dentistry da Nursing Science da Pharmacy da Medical Laboratory Science da Physiotherapy da Radiography da Optometry da Anatomy da kuma fannin Physiology, da kuma wasu sauran fannonin likitanci da kiwon lafiya da aka amince da su.
Sai dai duk da haka, an gindaya wasu sharuɗɗa da dole sai ɗalibi ya cika su kafin ya samu cancantar samun wannan tallafi, sharuɗɗan sun ƙunshi:
Dole ne ɗalibi ya kasance ɗan asalin Jihar Katsina ne, kuma ya kasance ɗalibi ne a ɗaya daga cikin jami'o'in Nijeriya da aka amince da su. Dole ne ɗalibi ya zamo yana karatun wani fanni da ya shafi likitanci ko kiwon lafiya da aka amince da shi. Sannan dole ne sai yana da ingantaccen lambobin katin zama ɗan ƙasa (National Identification Number (NIN). Daga ƙarshe dole ya tanaji cikakkun takardun shaidar karatu da na tantancewa domin cin gajiyar wannan tallafin.
Ibrahim Masari, bai yi ƙasa a gwiwa ba, sai da ya fito tare da yin cikakken bayanin yadda za a nemi tallafin kamar haka:
Za a gudanar da neman tallafin ne ta hanyar amfani da yanar gizo, wadda ba dole sai mutum ya buɗe account ba kafin neman tallafin. Za a iya cika neman tallafin kai tsaye a liƙau da ke ƙasa kamar haka: https://ikmss.com/