Iyalan EL-RUFAI Sun Ba Ministan Tsaro Musa Wa'adin Kwanaki 7 da Ya Janye Kalamansa Kan Zargin Shirya Kashe-Kashe, Ko Ya Fuskanci Shari'a

Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna kuma tsohon Ministan Birnin Tarayya (FCT), Malam Nasir Ahmad El-Rufai, sun ba Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), wa'adin kwana bakwai da ya janye kalaman da ya yi tare da ba da haƙuri a fili, game da zargin cewa El-Rufai ya shirya kashe-kashe a Kudancin Kaduna.

A cikin wata sanarwa da suka fitar a Abuja, iyalan sun gargaɗi Ministan Tsaron cewa idan ya gaza kafa hujja da tabbatattun shaidu ko kuma ya janye kalaman nasa a tsawon kwana bakwai, za su zamo ba su da wani zaɓi da ya wuce ɗaukar matakin shari'a.

Sanarwar, wadda Hon. Mohammed Bello El-Rufai ya saka wa hannu a madadin iyalan, ta fito ne a matsayin martani ga kalaman da Janar Musa ya yi, yayin da yake magana a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television. 

A yayin shirin, Ministan Tsaron ya yi zargin cewa El-Rufai ya gudanar da shirin kashe-kashe a Kudancin Kaduna a lokacin da yake gwamna.

Yayin da suke ayyana wannan zargi a matsayin mai nauyin gaske kuma mara tushe, iyalan sun bayyana cewa Janar Musa ya gaza gabatar da wata shaida mai goyon bayan kalaman nasa a yayin gudanar da shirin.

"Koda yake Janar Musa (mai ritaya) yana da haƙƙin faɗar ra'ayinsa na ƙashin kai, iyalan El-Rufai ma suna da haƙƙin buƙatar a kafa hujja da tabbatattun shaidu kan irin wannan zargi mai nauyi," cewar sanarwar.

Bugu da ƙari, iyalan sun buƙaci ministan da ya janye zargin a fili ta hanyar amfani da kafa guda da ya yi amfani da ita wajen fitar da kalaman.

"Sakamakon haka, an ba Janar Musa (mai ritaya) wa'adin kwana bakwai (7) daga ranar da aka fitar da wannan sanarwa, ko dai ya gabatar da hujjar goyon bayan zargin nasa ko kuma ya ba da haƙuri tare da janye kalaman gaba ɗaya a fili. Idan ya gaza yin hakan, iyalan za su zamo ba su da wani zaɓi face bin duk wata hanyar shari'a da doka ta tanada," in ji iyalan.

Malam Nasir El-Rufai, wanda ya yi gwamnan Jihar Kaduna tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, a yanzu haka yana ɗaya daga cikin shugabannin jam'iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC). Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Ma'aikatar Tsaro ba ta riga ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba game da buƙatar iyalan.

Post a Comment

Previous Post Next Post