Gwamnatin Tarayya ta fitar da sakamakon Jarabawar Shiga Kwalejojin Gwamnatin Tarayya (National Common Entrance Examination) ta shekarar 2026, inda ɗalibai 10 suka zama kan gaba bayan kowannensu ya samu maki 202 cikin maki 210 da ake iya samu.
Ƙaramin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmad, ta sanar da fitar da sakamakon a ranar Alhamis a Abuja bayan ta karɓi rahoton jarabawar daga Hukumar Shirya Jarabawa ta Ƙasa (NECO).
Ta bayyana cewa ɗalibai 70,357 ne suka yi rajistar shiga jarabawar neman gurbin karatu a Kwalejojin Gwamnatin Tarayya (FGCs) guda 80 da ke faɗin ƙasar.
A cewarta, ɗalibai 66,950 ne suka rubuta jarabawar da aka gudanar a ranar Asabar, 6 ga Yunin 2026, a Najeriya da kuma ƙasashen Jamhuriyar Benin da Togo, yayin da ɗalibai 3,407 ba su halarta ba.
Ta ce ɗalibai 10 da suka fi kowa ƙwazo sun samu maki 202 kowannensu, yayin da ɗalibai 82 suka samu mafi ƙarancin maki guda ɗaya.
Ministar ta ce ana gudanar da wannan jarabawa duk shekara domin bai wa yara ‘yan Najeriya da suka cancanta, ciki da wajen ƙasa, damar neman gurbin karatu a Kwalejojin Gwamnatin Tarayya da ke sassa daban-daban na ƙasar.
Farfesa Suwaiba Ahmad ta ƙara da cewa jarabawar ita ce ƙofar shiga aji na ɗaya na makarantar sakandare (JSS1) a Kwalejojin Gwamnatin Tarayya, tare da jaddada cewa tana daga cikin jarabawar shiga makaranta mafi tsauri da gasa a Najeriya.