'Yan Sandan Katsina Sun Sake Kama Karin Mutane Biyu da Ake Zargi da Karkatar da Abincin Tamowa

Jami'an Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina sun ƙara kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajan haɗa baki da kuma karkatar da abincin mai gina jiki na maganin yara da aka fi sani da 'Yar Kwamaso (RUTF) ba bisa ƙa'ida ba.

Mutanen da ake zargin, waɗanda aka gano sunansu Buhari Idris mai shekaru 40, da Idris Abdullahi Halliru mai shekaru 51, an kama su ne sakamakon wani bincike da aka gudanar inda aka same suna kasuwanci da kayan tallafin lafiyar al'umma ta hanyar da ta saɓa wa doka.

Kamun nasu ya biyo bayan wani samame da jami'an sintiri daga Rukunin Ɓatagarawa suka yi a ranar 26 ga Agusta, 2026, inda suka kama wani Mahmud Aliyu ɗauke da buhuna uku (sachets) na 'Yar Kwamaso, da aka sace, kimanin guda 1,500.

Yayin da ake gudanar da tambayoyi, Aliyu ya ambaci sunan Zaharaddini Musa, wani ma'aikacin asibiti wanda a halin yanzu yake a ɓoye.
Yayin da yake tabbatar da sabbin kamun a wata sanarwa a ranar Laraba, Jami'in Hulɗa da Jama'a na Rundunar 'Yan Sanda (PPRO), DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa tsawon mutane uku ne ke tsaye a hannun 'yan sanda a halin yanzu, kuma za a kai su kotu da zarar an kammala bincike.

Shi dai wannan abinci na RUTF, wani nau'in abinci ne na musamman na magani da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ke samarwa kyauta, tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran hukumomin tallafi na ƙasa da ƙasa. An ƙera shi ne musamman don jinyar yaran da ke fama da matsanancin ciwon tamowa waɗanda shekarunsu ba su kai biyar (5) ba, kuma an tanaje shi ne kaɗai don rarrabawa a ƙarƙashin kulawar likitoci a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

Yayin da take ba da gargaɗi mai tsauri ga ma'aikatan lafiya da sauran jama'a game da satar, siyarwa, ko rarraba kayan tallafin agaji ba tare da izini ba. Rundunar ta jaddada cewa, duk wanda aka kama da karkatar da kayan tallafi masu muhimmanci zai fuskanci sakamako mai tsanani a dokance.

"RUTF ba na siyarwa ba ne kwata-kwata. Abinci ne na musamman na magani da aka tanada kawai don yara masu rauni da ke fama da tamowa," in ji DSP Aliyu. "Duk wanda aka kama yana sana'a da shi, yana siye, ko yana siyarwa, ko yana amfani da shi ba bisa ƙa'ida ba, za a kama shi kuma a gurfanar da shi gaban shari'a bisa cikakken tsarin doka."

Yayin da yake sake jaddada matsayin Rundunar, Kwamishinan 'Yan Sanda, CP Ali Umar Fage, ya tabbatar da aniyar rundunar na kare kayan tallafin gwamnati da na hukumomin agaji da aka tanada don mutane masu rauni, tare da kiran mambobin jama'a da su kai rahoton duk wani al'amari na zargi ko karkatar da kayan agaji zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa.

Post a Comment

Previous Post Next Post