Gwamna Uba Sani, Ya Kaddamar da Manyan Tituna a Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan tituna da suka haɗa da hanyar Zango Road zuwa Asibitin Yara da sauran manyan hanyoyi a yankin kasuwar Panteka ta jihar Kaduna, hanyoyin suna daga cikin hanyoyi 160 masu tsawon kilomita 1,355 da Gwamnatin ke kan ginawa a jihar.

Ƙaddamar da waɗannan tituna na nuna ci gaba da ƙudirin gwamnatin jihar wajen faɗaɗa hanyoyin mota, inganta zirga-zirga, rage cunkoson ababen hawa da kuma sauƙaƙa rayuwar al’umma.

Tun bayan hawansa mulki, gwamnatin Uba Sani ta fara aikin gina sabbin hanyoyi 160 masu tsawon kilomita 1,355, inda aka fi mayar da hankali kan yankunan karkara da unguwannin marasa galihu domin tabbatar da ci gaba ya kai ga kowane ɓangare na jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post